Man United 0-1 Man United ta yi rashin nasara a gida a hannun Arsenal

Man United Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Manchester United ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Arsenal a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a filin wasa na Old Trafford.

Arsenal ta ci kwallon ne ta hannun Pierre-Emerick Aubameyang a bugun fenariti bayan Paul Pogba ya yi wa Hector Bellerin keta a da'irar yadi na 18.

Rabon da kyaftin din Arsenal ya ci kwallo a Premier League tun karawa biyar baya, wato tun cin Fulham ranar 12 ga watan Satumba.

Kawo yanzu an ci United kwallo biyar a bugun fenariti bakwai a wasan Premie League bakwai da ta yi a gida.

Daga cikin bakwai din, a wasa 101 ne aka doke ta a bugun fenariti biyar a filinta na Old Trafford.

Haka kuma Manchester United ta yi rashin nasara a gida a hannun Arsenal a gasar Premier League a karon farko tun Satumbar 2006 bayan karawa 13 ba ta yi rashin nasara ba, inda ta ci takwas da canjaras biyar.

Kuma wannan ne karon farko da Arsenal ta yi nasara a waje a kan manyan kungiyoyi shida a Premier League tun bayan 2-0 da ta doke Manchester City a Janairun 2015.

Wannan ne wasa na 100 da Ole Gunner Solskjaer ya ja ragamar Manchester United, inda ya ci wasa 55 da canjaras 21 da rashin nasara a fafatawa 24 kenan.

Da wannan sakamakon Arsenal ta yi sama zuwa mataki na takwas a kan teburi da maki 12, ita kuwa United tana na ta 15 a kan teburi da maki bakwai.

Wasa biyar nan gaba da Arsenal za ta buga:

Alhamis 5 ga watan Nuwamba Europa League

  • Arsenal da Molde

8 ga watan Nuwamba Premier League

  • Arsenal da Aston Villa

22 ga watan Nuwamba Premier League

  • Leeds da Arsenal

26 ga watan Nuwamba Europa League

  • Molde da Arsenal

28 ga watan Nuwamba Premier League

  • Arsenal da Wolves

Karawa biyar da ke gaban Manchester United:

Laraba 4 ga watan Nuwamba Champions League

  • Basaksehir da Man United

7 ga watan Nuwamba Premier League

  • Everton da Man United

Asabar 21 ga watan Nuwamba Premier League

  • Man United da West Brom

Talata 24 ga watan Nuwamba Champions League

  • Man United da Basaksehir

Lahadi 29 ga watan Nuwamba Premier League

  • Southampton da Man United