Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ozil, Solskjaer, Pereira, Griezmann, Burt

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan Arsenal Per Mertesacker ya ce hankalin dan wasan Jamus Mesut Ozil ya bar harkokin kwallon kafa - an cire dan wasan mai shekara 32 daga cikin tagawar Arsenal ta wasan Firimiya ranar Talata. (Klick and Rush podcast via Mail)
Tsohon dan wasan Manchester United Rio Ferdinand ya yi amannar cewa Ole Gunnar Solskjaer bai ji dadin yadda hukumar zartarwar kungiyar ta ki bari ya dauki 'yan wasan da yake so ba a lokacin musayar 'yan kwallo. (BT Sport via Express)
Tottenham ta kusa kulla yarjejeniyar dogon zango da dan wasan Koriya ta Kudu mai shekara 28 Son Heung-min. (The Athletic - subscription only)
ShugabanWatford Scott Duxbury ya ce dan wasan Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 22, da dan wasan Ingila Troy Deeney, mai shekara 32, sun sha alwashin taimaka wa kungiyar ta koma Gasar Firimiya. (London Standard)
Tsohon dan wasan Celtic da Rangers Liam Burt, mai shekara 21, ya je Pittodrie domin kallon fafatawar Aberdeen da Hamilton na Premiership a yayin da yake neman kungiyar da zai yi mata aiki. (Daily Record)
Dan wasan Portugal Ricardo Pereira, mai shekara 27, wanda aka yi wa tiyata a gwiwa, yana fatan komawaLeicester City don murza leda nan da mako shida. (O Jogo via The Independent)
Kungiyar kwallon kafarAZ Alkmaar ta ce 'yan wasa 13 sun kamu da cutar korona, ko da yake ta kara da cewa za ta fafata da Napoli a gasar Europa League ranar Alhamis kamar yadda aka tsara trun da farko. (Mail)
Dan wasanBarcelona dan kasar Faransa Antoine Griezmann, mai shekara 29, ya ce a shirye yake a rage masa albashi. (Marca)
Minista Vincenzo Spadafora ya soki dan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, saboda komawa Italiya daga Portugal bayan ya kamu da cutar korona. (Gazzetta dello Sport - in Italian)











