Premier League: Liverpool ta kasa cinye Everton a wasan hamayya

Everton ta riƙe Liverpool a Goodison Park inda ta ci gaba jan ragamar teburin Premier da tazarar maki uku.

Everton ta yunƙura tare da farke ƙwallo biyu a karo biyu a wasan hamayyar birnin Liverpool da ake yi wa laƙabi da Merseyside Derby tsakaninta da Liverpool.

Sadio Mane ne ya fara ci wa Liverpool ƙwallo minti uku da fara wasa a Goodison Park.

Sai dai Everton wadda ta lashe dukkanin wasanninta bakwai na baya-bayan nan, ta fusata tare da farke ƙwallon yayin da Michael Keane ya sara ƙwallo cikin ragar Adrián bayan James Rodríguez ya kwaso kwana.

Liverpool, tare da Thiago Alcantara a matsayin bakaniken aiki, ta sake jan ragamar wasan ana saura minti 18 a tashi lokacin da Mohamed Salah ya ɗaɗa ƙwallo a ragar Pickford.

Ba a tashi ba sai da Dominic Calvert-Lewin ya yi tsallen baɗake ya jefa ƙwallonsa ta bakwai a wannan kakar ana saura minti tara a busa tashi.

Na'urar VAR ta haramta wa Liverpool ƙwallon da ta zira a ragar Everton ana dab da hure wasa.

Everton ta riƙe Liverpool ne duk da an ba ɗan wasanta Richarlison jan kati bayan ya yi wa Thiago ƙeta.

Da wannan sakamako, Everton ta ci gaba da zama a matsayinta na ɗaya da maki 13 cikin wasa biyar, yayin da Liverpool ke biye mata da maki 10 cikin wasa biyar.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya yaba da yadda ƴan wasansa suka taka leda. "wannan ne wasa mafi kyau da muka buga a waje," in ji shi.

Everton ta kasa doke Liverpool a haɗuwa 23 da suka yi.

A wasan Everton na gaba, za ta kai ziyara ne gidan Southampton ranar Lahadi, yayin da kuma Liverpool za ta fafata da Amsterdam a gasar zakarun Turai ta Champions League a ranar Laraba kafin ta karɓi bakuncin Sheffield United a Premier League ranar Lahadi.