Kevin de Bruyne: Dan wasan Man City ba zai fafata ba a wasan da za su yi da Arsenal

Dan wasan Manchester City Kevin de Bruyne ba zai fafata a karawar da za su yi da Arsenal ranar Asabar ba a gasar Firimiya saboda raunin da ya ji.

An cire dan wasan dan kasar Belgium, mai shekara 29, daga wasan da kasarsa ta yi da Ingila na gasar Nations League ranar Lahadi.

Kocin Belgium Roberto Martinez ya ce ya dauki matakin ne "domin gudun abin da ka je ya zo," amma kocin City Pep Guardiola ya ce dan wasan ba zai buga wasan da za su yi da misalin karfe biyar da rabi na yammaci ba.

"Ina ganin ba wani abu ne babba ba, amma dai ina tsammanin ba zai buga wasannin da ke tafe ba. Za mu ga yadda za ta kaya," in ji shi.

De Bruyne ya koma City bayan ya bar tawagar Belgium kafin fafatawarsu da Iceland ranar Laraba.

City ita ce ta 14 a kan teburin Firimiya inda suka samu maki hudu a wasanni ukun farko da suka murza.

"Ban taba yin korafi ba kan hutun da 'yan wasa ke tafiya kasashensu don murza leda," a cewar Guardiola.

"Na san muhimmanci barin 'yan wasa su tafi kasashensu. Hakan wata martaba ce da kuma babbar dama. Ko da yaushe muna so 'yan wasa su dawo cike da kuzari, ba tare da sun ji rauni ba. Sai dai a wasu lokutan hakan ba zai faru ba."

Sai dai akwai labari mai dadin ji a kunnuwan Guardiola akan 'yan wasan da ke jinya, inda ake sa ran Sergio Aguero zai dawo daga doguwar jinyar da ya yi.

Dan wasan mai shekara 32 dan kasar Argentina ya ji rauni a wasan da suka fafata da Burnley ranar 22 ga watan Yuni, don haka bai buga karawar da City ta yi a Firimiya, da, FA Cup da kuma Zakarun Turai, da ma wasannin farko na kakar wasan bana.

"Ya kwashe kwana uku zuwa hudu yana atisaye. Yana atisaye ba tare da wata matsala ba. Ina farin cikin ganinsa bayan tsawon lokaci. Duk kungiya tana bukatar dan wasan gaba," in ji Guardiola.