Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Pogba, Alaba, Cantwell, Benrahma, Rose, Clyne
Barcelona na shirin dauko dan wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba da dan wasan Bayern Munich dan kasar Austria David Alaba, mai shekara 28. (Mundo Deportivo - in Spanish)
A gefe guda, Pogba mai shekara 27, yana ci gaba da samun goyon bayan mahukuntan Manchester United duk da cewa ya bayyana aniyarsa ta tafiya Real Madrid. (Manchester Evening News)
Golan Manchester United dan kasar Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, yana so a kyale shi ya yi gaba a karshen watan nan kuma an ce yana sha'awar murza leda a Amurka. (Sun)
Leeds United na son dauko dan wasan Norwich City da Ingila wanda ke murza leda a rukunin 'yan kasa da shekara 21 Todd Cantwell, mai shekara 22, da kuma dan wasan Derby County da Ingila Louie Sibley, mai shekara 19. (Yorkshire Evening Post)
West Ham ta kulla yarjejeniyar £30m da Brentford domin dauko dan wasan gaba Said Benrahma, mai shekara 25, amma dole su amince kan wata yarjejeniyar da dan wasan gaban na Algeria. (Sky Sports)
Middlesbrough na shirin dauko dan wasan Ingila da Tottenham Danny Rose, mai shekara 30, nan da ranar Juma'a da maraice. (Football Insider)
Crystal Palace ta kusa kammala kulla yarjejeniyar gajeren lokaci da dan wasa Nathaniel Clyne, mai shekara 29, wanda ba shi da kungiya tun da ya bar Liverpool a bazara. (The Athletic)
Cardiff da Swansea suna fafatawa a yunkurin dauko aron dan wasan Liverpool dan yankin Wales Harry Wilson, mai shekara 23, don yin zaman kakar wasa daya. (Wales Online)
Dan wasanManchester United da Sifaniya Juan Mata, mai shekara 32, ya yi watsi da tayin tafiya wata kungiyar Saudiyya inda za a rika biyansa £200,000 duk mako. (Sport)
Manchester Unitedna sanya ido kan dan wasanSevilla da Faransa Jules Kounde, mai shekara 21, gabanin bude kasuwar 'yan wasa ta watan Janairu. (ESPN)
Tsohon dan wasan Manchester City da Liverpool Mario Balotelli, mai shekara 30, wanda ba shi da kungiya tun da ya bar Brescia, zai tafi sabuwar kungiyar "nan da 'yan makonni kadan masu zuwa". (Goal)