Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Benrahma, King, Tagliafico, Skriniar, Camavinga
West Ham tana jan kafa kan shirinta na sayen dan wasanAlgeria Said Benrahma a kan £25m daga Brentford inda yanzuta mayar da hankali wurin dauko dan wasan Bournemouth dan kasar Norway Josh King, mai shekara 28. Crystal Palace tana iya soma zawarcin Benrahma, mai shekara 25. (Mirror)
Manchester City za ta sake yunkurin dauko dan wasan Ajax da Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 28, a watan Janairu. (Sun)
Mai yiwuwa Tottenham ta farfado da sha'awarta ta dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, a watan Janairu. (Team Talk)
Manchester United ta "dauki matakai" da za su kai ta ga daukar dan wasan Rennes da Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 17, idan dan kasarsa Paul Pogba, mai shekara 27, ya yanke shawarar barin Old Trafford. (Sport Witness)
Manchester United tana iya fuskantar kalubale daga Real Madrida yunkurin dauko Camavinga. (Star)
Tattaunawar daFulham take yi ta yi nisa a yunkurin dauko dan wasan Huddersfield dan kasar Netherlands Terence Kongolo, mai shekara 26. (Football Insider)
'Yan wasan Manchester United da dama sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda ake 'wulakanta' gola Sergio Romero, mai shekara 33, dan kasar Argentina wanda aka yi watsi da shi a Old Trafford tun bayan komawar Dean Henderson kungiyar kuma bai samu damar barin kungiyar ba har aka rufe kasuwar musayar 'yan kwallo saboda United ta dage cewa sai an biya ta kusan £10m kafin ya tafi. (ESPN)
Mahaifin dan wasan Arsenal da Ghana mai shekara 27, Thomas Partey, ya yi ikirarin cewa dansa yana jiran tayi daga "manyan kungiyoyi" a yayin da Juventus da Chelseasuke zawarcinsa. (Mirror)
An biya dan wasanArsenal Mesut Ozil, mai shekara 31, wanda bai murza wa kungiyar leda ba tun watan Maris, alawus £8m a karshen watan Satumba. (The Athletic - subscription required)
Dan wasan Faransa Frederic Guilbert, mai shekara 25, ya sha alwashin samun wurin zama aAston Villa bayan ya bayyana cewa ya gaza tafiya Nantes a lokacin musayar 'yan kwallo. (Express and Star)
Tsohon dan wasan Manchester City da Brazil Robinho, mai shekara 36, ya amince ya karbi albashin £200 duk wata a yayin da ya koma kungiyarsa ta farko Santos karo na hudu. (Manchester Evening News)