Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar korona
Hukumar kula da kwallon kafar Portugal ta ce dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar korona.
Dan wasan mai shekara 35 ba ya nuna wata alama ta kamuwa da cutar ba kuma an aika da shi gida domin ya killace kansa.
Portugal za ta fafata da Sweden a matakin rukuni na Nations League ranar Laraba.
Gwajin da aka yi wa sauran 'yan wasan tawagar Portugal wadda Fernando Santos ke jagoranta ya nuna cewa ba su kamu da cutar ba don aka za a iya zabensu don fafatawa a wasan.
Portugal da Faransa sun tashi babu ci a fafatawar da suka yi ranar Lahadi a Paris kuma su ne kan gaba a rukuninsu.
Kazalika Juventus za ta fafata da Verona ranar 25 ga watan na Oktoba.
Cristiano Ronaldo ya zama dan kasar Turai na farko da ya zura kwallo fiye da 100 a wasan da aka fafata da wata kasa rukunin kwallon kafar maza kuma ya zarta wannan adadi bayan ya ci kwallo biyu a gasar Nations League inda suka yi nasara a kan Sweden a watan Satumba.
Watakila Ronaldo ba zai fafata a karawar da Juventus za ta yi a Crotone ta gasar Serie A ba ranar 17 ga watan Oktoba da kuma wanda za su yi da Dynamo Kiev a matakin rukuni na gasar Champions League ranar 20 ga watan na Oktoba.