Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kevin de Bruyne: Dan wasan Manchester City ba zai yi wa tawagar Belgium wasa ba
Kevin de Bruyne ya bar sansanin tawagar kwallon kafa ta Belgium, ba zai buga wasan da za ta yi da Iceland ba ranar Laraba, har ya koma Manchester City.
An sauya dan kwallon mai shekara 29 a minti na 73 a gasar Nations League da Ingila ta yi nasara da ci 2-1 a Wembley.
Tawagar Belgium tana ta biyu a teburin da Ingila ke jan ragama da maki daya tal tsakani a gasar ta Nations League, bayan buga wasa na uku-uku.
Manchester City za ta buga karawar gaba a gasar Premier League da Arsenal a Etihad ranar Asabar.
Bayan da aka tashi wasan da Ingila ta yi nasara a kan Belgium, koci Roberto Martinez ya ce ya sauya De Bruyne ne domin ya huta kuma kar ya ji rauni.
De Bruyne zai bi sahun Raheem Sterling - wanda bai buga wa Ingila wasa ba - da ake cewar da kyar idan zai fafata a karawa da Arsenal din.
Manchester City tana mataki na 14 a kasan teburin Premier League ta bana da maki hudu a wasa ukun da ta buga kawo yanzu.