Edinson Cavani: Ba zai je wasan da Man Utd za ta ziyarci Newcastle ba

Sabon dan wasan da Manchester United ta dauka Edinson Cavani ba zai buga karawa da Newcastle ranar Asabar a gasar Premier League ba, saboda killace kansa da ya yi a kungiyar.

Dan kwallon Uruguay ya koma Old Trafford a makon jiya, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St-Germain a karshen kakar bana.

Sai a ranar Talata dan wasan mai shekara 33 zai buga Champions League da United za ta yi da tsohuwar kungiyarsa, bayan ya kammala killace kansa.

Tun cikin watan Maris rabonda Cavani ya yi atisaye tare da 'yan wasa.

Dan kwallon ya killace kansa da aka bukaci mako biyu, bayan da ya isa Ingila daga Faransa ranar 4 ga watan Oktoba.

Haka kuma Manchester United za ta je St James Park ba tare da Anthony Martial ba, bayan da aka ba shi jan kati a karawa da Tottenham a Old Trafford.

Wasannin Premier League da za a ci gaba da buga wa:

Ranar 17 ga watan Oktoba

Everton da Liverpool

  • Chelsea da Southampton
  • Manchester City da Arsenal
  • Newcastle United da Manchester United

Ranar 18 ga watan Oktoba

  • Sheffield United da Fulham
  • Crystal Palace da Brighton & Hove Albion
  • Tottenham da West Ham United
  • Leicester City da Aston Villa

Ranar 19 ga watan Oktoba

  • West Bromwich Albion da Burnley
  • Leeds United da Wolverhampton Wanderers