Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Aguero, King, Benrahma, Depay

Asalin hoton, Reuters
Kocin Inter Milan Antonio Conte zai soma shirin dauko dan wasan Manchester City dan kasar Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, wanda kwangilarsa za ta kare a karshen kakar wasan da muke ciki. (Calciomercato)
Bournemouthta ki amincewa da tayin daWest Ham ta yi mata na biyan £13m don dauko dan wasan Norway Joshua King, mai shekara 28. (Mail)
West Ham na ci gaba da tattaunawa da zummar dauko dan wasan Brentford dan kasar Algeria Said Benrahma, mai shekara 25. (Evening Standard)
Everton tana son dauko dan wasan Bournemouth King. (Talksport)
Tsohon dan wasan Manchester United Memphis Depay bai cire ran tafiya Barcelona ba a watan Janairu. Dan wasan na Netherlands ya zauna a Lyon domin kammala kwangilarsa bayan Barca ta nuna sha'awar daukar sa a bazarar da ta wuce sai dai Lyon za ta iya jinkirta sayar da dan wasan mai shekara 26 sai lokacin musayar 'yan kwallo mai zuwa. (Marca)
Sabon dan wasan da United ta saya Facundo Pellistri, dan kasar Uruaguay mai shekara 18, ya soma tattara kayansa domin komawa kungiyar kasarsa Penarol, wato kungiyar da ya bar ta ya tafi Old Trafford. (Sun)
Manchester City ta yanke shawarar rike dan wasan Sufaniya Eric Garcia tsawon kakar wasa daya saboda darajarsa ta fi ta £18m da Barcelona ta mika mata don daukarsa, a cewar babban jami'in kungiyar Omar Berrada. Garcia, mai shekara 19, zai iya tafiya Nou Camp ba tare da ko sisi ba a bazara mai zuwa bayan ya ki sabunta zamansa. (Manchester Evening News)
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ce da ya kamata dan wasan Uruguay Luis Suarez, mai shekara 33, ya zauna a kungiyar domin ya nuna masa cewa zai iya murza ledar da yake so maimakon ya tafi Atletico Madrid.(Goal)
Tsohon dan wasan Liverpool da Ingila Daniel Sturridge, mai shekara 31, ya yi amannar cewa babu shakka zai koma fagen tamaula, bayan kashe aurensa da kungiyar Trabzonspor ta kasar Turkiyya a watan Maris, a ranar da aka haramta masa buga kwallon duniya tsawon wata hudu saboda karya doka. (Liverpool Echo)
Dan wasan Denmark Joachim Andersen ya ce manaja Scott Parker ya lallabe shi ya koma Fulham. Torino ta dade tana zawarcin dan wasan mai shekara 24. (90 Min)
Dan wasan Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22, ya yi amannar cewa shawarar da ya yanke ta zama a Lyon a wannan bazarar za ta kasance mafi alheri bayan da aka rika rade radin zai tafi Arsenal.(Telefoot, via Mail)











