Ansu Fati: Karon farko da ya lashe gwarzon dan kwallon La Ligar Spain

Ansu Fati

Asalin hoton, Getty Images

An bayyana dan kwallon Barcelona, Ansu Fati a matsayin gwarzon dan wasan La Liga na watan Satumba.

Masu bibiyar gasar La Liga da wadanda ke daukar nauyin gasar ne wato Santander suka gudanar da zaben da ya sa Fati ya zama fitaccen a watan Satumba.

Ɗan wasan Mai shekara 17 ya ci wa Barcelona kwallo uku a wasa biyu da fara kakar bana har da biyu da ya zura a ragar Villareal a Camp Nou.

Shi ne ya fara cin Celta Vigo a karawar mako na uku a gasar La Liga da Barcelona ta yi nasara da ci 3-0 ranar 1 ga watan Oktoba.

Sai dai kuma bai ci kwallo ba a wasa na uku da ya buga wanda Barcelona ta tashi 1-1 da Sevilla a Camp Nou ba, inda Luuk de Jong ne ya fara cin kwallo, Philippe Coutinho ya farke minti biyu tsakani.

Ansu Fati ya yi takara ne a kyautar gwarzon watan Satumba tare da dan wasan Celta Iago Aspas da na Atletico Madrid Luis Suarez da na Real Betis Sergio Canales da na Levante Jose Luis Morales da na Real Sociedad Mikel Merino da kuma Luis Milla na Granada.

Kwallo ukun da ya ci a gasar La Liga ya sa ya yi kan-kan-kan da wadanda suka zura uku a raga kawo yanzu tare da Aspas da Morales da Maxi Gomez da Paco Alcacer da kuma Gerard Moreno.

A Barcelona kuwa Ansu Fati shi ne kadai ya ci wa kungiyar kwallo sama da daya a bana sai Lionel Messi da Sergi Roberto da kuma Philippe Coutinho da kowanne ya ci ɗaya.

Haka kuma sabon dan kwallon tawagar Spain shi ne dan wasan Barcelona bayan Messi da Suarez da ya karɓi kyautar, tun bayan Neymar da ya yi bajinta a Nuwambar 2015.

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Waɗanda ke kan gaba a lashe kyautar gwarzon La Liga ta wata-wata

  • Lionel Messi 7
  • Antoine Griezmann 6
  • Luis Suarez 4
  • Cristiano Ronaldo 3
  • Aspas 3
  • Aritz Aduriz 2
  • Karim Benzema 2
  • Diego Godin 2
  • Koke 2
  • Nolito 2
  • Carlos Vela 2

Ranar da za a ci gaba da wasannin La Liga:

Karawar mako na shida

Asabar 17 Oktoba

  • Granada da Sevilla
  • Celta Vigo da Atletico Madrid
  • Real Madrid da Cadiz
  • Getafe da Barcelona

Sunday 18 Otoba

  • SD Eibar da Osasuna
  • Athletic Bilbao da Levante
  • Villarreal da Valencia
  • Deportivo Alaves da Elche
  • Huescada Real Valladolid
  • Real Betis da Real Sociedad