Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Alli, Aouar, Rudiger, Torreira, Gray

Tottenham ta ki amincewa da tayin £1.5m daga wurin Paris St-Germain domin karbar aron dan wasan Ingila Dele Alli saboda haka dan wasan mai shekara 24 zai ci gaba da zama a Ingila. (Guardian)

Amma PSG tana sake shiri domin karbo aron Alli. (Telegraph)

A gefe guda, Tottenham ta nemai karbo aron dan wasan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, kuma an ce kungiyoyin biyu da ke hamayya sun soma tattaunawa kan hakan. (Nicolo Schira, via Express)

Arsenal ta amince ta bai wa Atletico Madrid aron dan wasan Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 24, kuma hakan zai ba ta damar dauko dan wasan Faransa mai shekara 22 Houssem Aouar daga Lyon. (AS, via Mirror)

Paris Saint-Germain za ta iya yin kafar-ungulu ga yunkurin Arsenal na dauko Aouar bayan da ita ma ta bi sahun tattaunawar dauko dan wasan na Faransa. (L'Equipe, via Metro)

Leicester City ta shirya sayar da dan wasan Ingila mai shekara 24 Demarai Gray, wanda yake shekarar karshe a kwangilarsa da kungiyar. (Mirror)

Inter Milan na shirin dauko dan wasan Chelseada Sufaniya mai shekara 29 Marcos Alonso. (Sky Sports)

Leicester City za ta sabunta kwangilar Harvey Barnes bayan da dan wasan mai shekara 22 ya samu cikakkiyar gayyatarsa ta farko domin fafatawa a tawagar kwallon kafar Ingila. (Telegraph)

Manchester United na yunkurin dauko dan wasan Atalanta da Ivory Coast Amad Traore, mai shekara 18. (Manchester Evening News)

Fulham na kokarin dauko 'yan wasa biyu da ke tsaron gida kafin a rufe kasuwar 'yab kwallo ranar 5 ga watan Oktoba, inda take sanya ido kan dan wasan PSV Eindhoven dan kasar Jamus Timo Baumgartl, 24. (Telegraph)