Man United: Ya kamata Man United ta kara karfin 'yan wasanta a bana

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Manchester United ta fara kakar bana ta Premier League da kafar hagu, bayan da Crystal Palace ta je Old Traford ta yi nasara da ci 3-1 a karawar makon farko.

United ta yi namijin kokari a kakar bara da ta kai samun gurbin buga Champions League, bayan da ta kare kakar a matsayi na uku a teburi, kuma hakan ne ya sa ake hasashen kungiyar za ta kara kaimi a shekarar nan.

Ko da ya ke United ta yi nasara a kan Brighton a wasan mako na biyu da ci 3-2, duk da cewa ta yi nasara amma barakarta ta bayyana a fili, domin sai a minti karshe kungiyar ta zura kwallo na uku a bugun fenariti.

United ce ta mamaye karawa da Brighton sai dai ta kasa zura kwallo a raga da hakan ke nuna karancin 'yan kwallon da ke da kwarewar bai wa 'yan gaba su ci kwallo.

Kungiyar ta Old Trafford na bukatar dan kwallon da ke wasa ta gaba daga gefen hagu ko kuma dama da zai zari kwallo ya keto ta tsakiya ya bayar a kuma zura a raga, kamar yadda Ryan Giggs ya yi.

Ko kuma a samu kwararre da zai dunga bugo kwallo daga gefen gaba ta zo wajen masu cin kwallo cikin sauki da su kuma daga buhu sai tukunya, idan ka tuna da David Beckham.

Wannan bangaren yadda za ta dunga cin kwallo kenan, duk da haka kungiyar na bukatar dan wasa kwararre mai buga tsakiya mai caji kamar yadda ya kamata mai kuma koshin lafiya da za a dade ana mora, ba mai yawan rauni ba.

Saboda haka wannan karon zan yi magana kan 'yan wasan da ke buga gefe daga gaba da ya kamata duk runtsi United ta dauka, daga baya mu leka tsakiyarta da masu tsaron baya.

Kowa ya san cewar mai tsaron ragar kungiyar kwararre ne wato David de Gea, sai dai duk kyan gola idan ba shi da tsakiya da masu tsare masa baya, sai kaga ya zama rariya kwallaye nata shiga raga.

Sai dai kuma duk wanda za a dauka zuwa United zai sa watakila tsakanin Mason Greenwood ko Marcus Rashford ko kuma Anthony Martial wani ya yi zaman benci.

Wanda ake cewa United za ta kara dauka a kakar bana shi ne Jadon Sancho koda yake har yanzu babu wani batun mai karfi da dan kwallon zai iya zuwa Old Trafford.

Idan har Sancho bai samu zuwa United ba watakila kungiyar ta dauki daya daga cikin wadan nan 'yan kwallon da suke taka rawar gani a kungiyoyinsu.

1. Sergio Canales

Dan kwallon Real Betis mai shekara 29 yana daga ciki wadanda ake ta rade-radin United za ta dauka. Ya dai samu cikas lokacin da Real Madrid ta dauke shi na rashin buga wasa sosai.

Yanzu kuma ya dawo Real Betis da taka leda, wanda yawanci yakan yi lamba 10 to amma yawo a tsakiya fili yana da amfani ta nan wajen.

Shi dai Canales bai yi fice wajen yanka ba kamar sauran 'yan wasan da aka lissafa, amma ya yi fice wajen bayar da damarmakin cin kwallo sai dai a samu matsala daga mai ci ba dai daga mai bayar da tamaula ba, a mafi yawan lokuta da ya baka bugawa za ka yi ta shiga raga.

Ko za ka yi tunani shi da Juan Mata ka hada su daya na hagu daya na dama sannan ka rage yawan wasan da Bruno Fernandes da kuma Paul Pogba.

Da zarar kana da Canales ba abinda koci zai yi illa yadda zai zakulo masu iya cin kwallo da zai dunga sa musu suna zurawa a raga, hakan sai kaga United ta yi fice a wasannin bana.

2. Lucas Ocampos

Dan kwallon da ya taka rawar gani a Uefa Super Cup da Bayern Munich ta yi nasara na daga cikin zakakuren da ke haskakawa a tamaula a Sevilla mai shekara 26 da za a moreshi ga duk kungiyar da ta dauke shi ba faduwa za kuma ta ci riba.

Ocampos ya kara nuna bajintarsa tun lokacin da Julen Lopetegui ya karbi jan ragamar Sevilla. Haka kuma dan kwallon kan buga wasa daga gefen gaba hagu ko dama ya kan ratso da kwallo tsakiya kamar yadda ake bukata a gasar Premier League.

Da zarar ya kwantar da hankalinsa a Ingila zai zama fitatcen da za a dade ana tunawa da shi, domin salon kwallonsa irin wadda ko wacce kungiya ke bukata.

Baya yawan dawo da kwallo baya da ya samu zai nufi mai tsaron baya ya kuma kware wajen rike tamaula da raba ta a lokacin da ya dace.

Dan kasar Argentina ya buga wasa 44 ya kuma ci kwallo 17 a kakar da ta wuce ya kuma karbi jan kati daya da katin gargadi wato mai ruwan dorawa 11.

Cikin kungiyoyin da ya buga wa tamaula sun hada da Monaco da Marseille da Genoa da Milan sannan ya koma Sevilla ranar 3 ga watan Yulin 2019.

3. Wilfried Zaha

Dan wasan Crystal Palace, Zaha shi ne ya fi dacewa da United ta dauka a bana, saboda sau biyu yana cin kwallo a Old Trafford a bana.

Hakika dan kwallon zai yi tsada, sai dai ba zai kai wadda Sancho zai kai ba, amma dai Zaha ya nuna yadda yake wasan kura da masu tsaron baya a gasar Premier ga yanka ga cin kwallo yana buga gefe yana kuma jan kwallo ya shiga da ita tsakiya, ko dai ya ci ko kuma ya bai wa abokan wasa.

Matsala guda Zaha keda ita ba ta wuce ta yawan satar gida ba da yakan yi a wasanninsa, amma dai yana daga kashin bayan Palace sannan ya san yadda ake buga gasar Premier League kuma kwararrene shi a fanni tamaula.

Dan wasan mai shekara 27 ya kware wajen yanka da samun fawul da ake yi wa yawan keta ya kuma iya cin kwallo kuma shi kadai ya ci fenariti bakawi a kakar 2018-19 ba dan wasan da ya yi wannan bajintar a shekarar.

4. Ivan Perisic

Dan kwallon Inter Milan mai shekara 31 ba a yi zawarcinsa kamar yadda kungiyoyi da dama suka yi a bara ba, an kuma sa ran kila tsohon kocinsa Jose Mourinho zai kai shi Tottenham amma dai shiru har yanzu.

Sai dai ya taka rawar gani a kakar da ta wuce domin dan kwallo ne mai sa kwazo da sai inda karfinsa ya kare, wanda ya dauki sana'arsa da mahimmaci matuka.

Kuma dan kwallon ne da ke amfani da dukkan kafafuwansa biyu yana kuma taka leda daga gefen hagu ko dama daga gaba ya kan yi wasan tsakiya.

Yana da dukkan kwarewar da United ke bukata illa dai shekaru sun ja, shi kuwa kocin kungiyar Old Trafford na gina ta da kananan yara da za a mora nan gaba kamar yadda Sir Alex Ferguson ya yi.

Wasannin gaba da United za ta buga

EFL Cup Laraba 30 ga Satumba 2020

  • Brighton da Man Utd

Premier League Lahadi 4 ga watan Oktoba 2020

  • Man Utd da Tottenham

Premier League Asabar 17 ga Oktoba 2020

  • Newcastle da Man Utd

Premier League Asabar 24 ga Oktoba 2020

  • Man Utd da Chelsea

Premier League Asabar 31 ga Oktoba 2020

  • Man Utd da Arsenal

Premier League Asabar 7 ga Nuwamba 2020

  • Everton da Man Utd

Duk da cewar gasar Premier League ba ta yi nisa ba, amma dai Palace ta fara karyawa da United a Old Trafford, ina kuma ga batun Liverpool ko kuma Leicester City wacce ta je ta doke Manchester City 5-2 a Etihad a karshen mako?

Akwai kuma kungiyoyi masu naci kamar Leeds United wacce ta yi kare jini biri jini da Liverpool da dai sauran kungiyoyi da dama.

Lokaci dai bai kurewa Manchester United ba domin tana da wasanni da dama a gabanta da suka hada da Premier League da Caraboa da FA da Champions da kuma Europa League, dole sai ta tashi tsaye yadda ya kamata.

Dan kwallon da United ta dauka a bana

  • Donny van de Beek daga Ajax kan fam miliyan 35,000,000

'Yan wasan da suka bar kungiyar a bana

  • Cameron Borthwick-Jackson zuwa Oldham
  • Angel Gomes zuwa Lille
  • Alexis Sanchez zuwa Inter
  • Ethan Hamilton zuwa Peterborough
  • Demetri Mitchell zuwa lackpool
  • Kieran O'Hara zuwa Burton