Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan da suka sa Suarez zai bar Barcelona zuwa Atletico
Bayan kaka shida da Luis Suarez ya yi a Camp Nou ya kuma lashe La Liga hudu da Champions League da cin ƙwallo 198, ɗan wasan zai koma Atletico Madrid a bana.
Suarez ya buga wa Barcelona wasa 36 a kakar 2019-20 ya kuma ci mata kwallo 21, sai dai ya yi fama da jinya.
A cikin watan Janairun 2020 sai da Suarez ya yi jinyar wata hudu, dalilin da ya sa dan wasan bai buga wa tawagar Uruguay karawar neman shiga kofin duniya a watan Maris ba.
Barcelona ta ƙarƙare kakar 2019-20 ba tare da lashe kofi ba, bayan da ta yi ta biyu a La Ligar da aka karkare wacce Real Madrid ta lashe.
Hakan ne ya sa kungiyar ta tsara shirye-shiryen da zai sa ta taka rawar gani a kakar 2020-21.
'Yan wasan da Barcelona ta dauka a bana
- Pedri Las daga Palmas
- Trincao daga Braga
- Matheus Fernandes daga Valladolid
- Miralem Pjanic daga Juventus kan fam miliyan 54,000,000
'Yan kwallon da suka bar Barcelona a bana:
- Marc Cucurella zuwa Getafe
- Guillem Jaime zuwa Castellon
- Ivan Rakitic zuwa Sevilla
- Arthur zuwa Juventus
- Dani Morer zuwa Famalicao
- Arturo Vidal zuwa Inter
- Jorge Cuenca zuwa Villarreal
Haka kuma Barcelona ta ɗauki sabon koci Ronald Koeman a bana, wanda ya fayyace ba zai yi aiki da dan kwallon tawagar Uruguay ba, duk da cewar Suarez na son ci gaba da zama a kungiyar koda zaman benci ne.
An yi ta rade-radin cewar kungiyoyi da dama na zawarcin tsohon ɗan ƙwallon Liverpool, kuma a wannan makon batun zuwansa Juventus ya bi ruwa saboda batun fasfo.
Suarez ya amince a rage masa albashi a ƙungiyar Atletico duk don ya bar Barcelona a bana, an kuma fahimci cewar shugaban Barcelona, Josep Maria bai so a sayar da dan kwallon ba.
Shugaban ya yi taro da wakilan Suarez kan cewar yana bukatar dan wasan ya ci gaba da zama a Barcelona, shi kuwa ɗan kwallon ya ce zai sanar da 'yan jarida halin da ake ciki kan batun barin kungiyar.
Kawo yanzu Atletico abokiyar hamayyar Barcelona za ta biya Suarez mai shekara 33 Yuro miliyan hudu, hakan ma idan kungiyar ta taka rawar gani a Champions League.
Suarez zai karbi rabin Yuro miliyan 30 a shekara a Atletico, abinda ake ba shi a Barcelona.
Dan kwallon na Uruguay ya koma Barcelona daga Liverpool shekara shida da suka wuce kan fam miliyan 74 daga Liverpool.
Ya kuma taka rawar gani a kungiyar ta Camp Nou da ya yi wasa 283 a lokacin da suka addabi duk kungiyo da suka hadu da ita a lokacin tare da Messi da Neymar.
Dan wasan ya lashe Copa del Rey hudu da kofin zakarun nahiyoyin duniya da ake kira Club World Cup a 2015.
Wasannin da Barcelona za ta fara buga wa a La Liga ta 2020-21:
Lahadi 27 ga Satumba 2020
- Barcelona da Villarreal
Laraba 30 ga Satumba 2020
- Celta Vigo da Barcelona
Lahadi 04 ga Oktoba 2020
- Barcelona da Sevilla
Lahadi 18ga Oktoba 2020
- Getafe da Barcelona