Luis Suarez: Barcelona ta amince ta sayar da ɗan wasan tsakiya ga Atletico Madrid

    • Marubuci, Daga Guillem Balague
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Marubucin labaran kwallon kafa a Sufaniya

Barcelona ta amince dan wasanta na tsakiya Luis Suarez ya tafi abokiyar hamayyarta a La Liga Atletico Madrid.

Barca ba ta bukatar Suarez kuma tana farin cikin sakinsa ba tare da ko sisi ba, amma idan ba zai tafi wasu kungiyoyi ba.

Dan wasan na Uruguay ya amince a rage albashinsa a Atletico bayan yunkurinsa na tafiya Juventus ya gagara saboda rashin samun fasfo.

Daga nan ne shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya hana shi tafiya saboda ba ya son sayar da dan wasan ga abokan hamayyarsu a Sufaniya.

Sai dai bayan tattaunawa da wakilan Suarez, yanzu Barca ta amince dan wasan ya tafi, saboda dan wasan ya yi barazanar shaida wa manema labarai halin da yake ciki.

Atletico za ta biya kusan euro 4m don karbar dan wasan mai shekara 33, kodayake za ta yi hakan ne idan ya taimaka mata ta samu gurbi a Gasar Zakarun Turai.

Suarez zai rika karbar euro 15m a Atletico, wato rabin kudin da ake ba shi a Barca.

Tafiyarsa Atletico za ta kawo karshen zaman shekara shida da Suarez ya kwashe a Barca, inda ya zura kwallo 198 a wasanni 283 da ya murza wa kungiyar kuma yana cikin 'yan wasa uku da aka fi tsoro wadanda suka hada da Lionel Messi da Neymar.

Ya je Barca daga Liverpool a 2014 a kan £74m kuma ya taimaka mata wajen lashe Kofin La Liga hudu, Kofin Copa del Reys hudu, Kofin Zakarun Turai daya da kuma Kofin Gasar Lig ta Duniya guda daya a 2015.