Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Pochettino, Foster, Gabriel, Kean, Hendrick, Smalling

Manchester City ta yi amannar cewa tana matsayin da ya fi dacewa ta dauko Lionel Messi domin su sake hadewa wuri guda da Pep Guardiola idan dan wasan na Argentine mai shekara 33 ya bar Barcelona, in ji jaridar Mirror.

Tsohon kocin Spurs Mauricio Pochettino yana kan gaba a cikin masu neman zama kocin Barcelona, a yayin da kungiyar ke shirin korar Quique Setien nan da kwanaki kadan masu zuwa, a cewar Guardian.

Chelsea da Everton suna zawarcin dan wasanWatford mai shekara 37 wanda kuma tsohon golan Ingile ne Ben Foster. (Sun)

Chelsea na dab da kulla yarjejeniya ta tsawon lokaci da dan wasa Ben Chilwell, mai shekara 23, daga Leicester. (Independent)

Tsohon kocinBournemouth Eddie Howe ba shi da niyyar komawa fagen tamaula sai bayan Kirsimeti domin yana son hutawa bayan barin Cherries. (Mail)

Dan wasanLille dan kasar Brazil Gabriel, 22, wanda ake rade radin zai tafi Manchester United ko Arsenal, zai bar kungiyar a bazarar nan, a cewar mamallakin kungiyar. (Goal)

Borussia Monchengladbach na shirin dauko dan wasan Lyon Maxwel Cornet, wanda ya zura kwallon farko a gasar zakarun Turai da suka yi nasara kan Manchester City, amma Wolfsburg na sondan kasar ta Ivory Coast mai shekara 23. (Le 10 Sport - in French)

Wakilin Moise Kean Mino Raiola yana kokarin ganin dan wasan mai shekara 20 ya tafi AC Milan. (Calciomercatoweb)

Dan wasan tsakiya Jeff Hendrick yana shirin sanya hannu kan kwangila a Newcastle United. Dan wasan a Jamhuriyar Ireland mai shekara 28 ya bar Burnley bayan kwangilarsa ta kare ranar 30 ga watan Yuni. (Talksport)

Dan wasan Manchester United Chris Smalling, mai shekara 30, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce a Roma, ba ya son tafiya St James' Park. (Mail)

Inter Milan na shirin kashe £20m don dauko dan wasan nan Ingila wanda zai iya hadewa da tsofaffin abokansa a United Romelu Lukaku da Alexis Sanchez. (Express)

Thiago Alcantara ya yi bankwana da abokansa na Bayern Munich a yayin da dan wasan na Sufaniya mai shekara 29 yake shirin tafiya Liverpool a bazarar nan.(Talksport)

An yi amannar cewa Napoli tana kan gaba a yunkurin dauko dan wasan Real Madrid dan kasar Sufaniya Sergio Reguilon, mai shekara 23, wanda yake zaman aro a Sevilla. (Calciomercato - in Italian)