An ƙi amincewa da tayin Manchester United kan Sancho, Coutinho zai yi nazari kan tafiya Arsenal

England winger Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

Borussia Dortmund ta ki amincewa da tayin da Manchester United ta yi na sayen dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, a kan £89m, a cewar mujallar wasanni ta Bild, wacce ta ambato jaridar Mail.

Sai dai jaridar (Telegraph ta ce har yanzu United ba ta mika bukatar dauko Sancho ba, kuma duk da cewa Dortmundna so a ba ta £110m kan dan wasan, wato sama da darajar da kungiyar ta Premier League ta yi a kansa, an yi amanna za a cimma matsaya. (Telegraph - subscription required)

Kocin Manchester United Ole Gunnar yana son dauko dan wasan Aston Villa Jack Grealish sai dai tuni aka gaya wa dan wasan na Ingila mai shekara 24 cewa da farko mai yiwuwa ba za a rika sanya shi a wasa duk mako ba idan ya tafi Old Trafford. (Independent)

Dan wasan tsakiya na LeicesterCity James Maddison, mai shekara 23, ya sabunta zamansa a a kungiyar zuwa shekarar 2024 kuma za a rika biyansa £110,000 duk mako. (Goal)

Chelseata soma tattaunawa daBayer Leverkusen a kan farashin dan wasan Jamus mai shekara 21 Kai Havertz bayan ta samu gurbin buga gasar Zakarun Turai mai zuwa. (Guardian)

Dan wasan Brazil Willian, mai shekara 31, zai iya amincewa da sabuwar yarjejeniya aChelsea kafin karshen makon nan bayan an cimma matsaya tsakaninsa da kungiyar a tattaunawar da suka yi. (Sky Sports)

Dan wasan Barcelona Philippe Coutinho ya gaya wa Arsenal ta ba shi karin lokaci domin ya yi nazari kafin ya yanke shawara kan makomarsa, inda rahotanni suka ce Leicester City da Tottenham suna son dauko dan wasan mai shekara 28 dan kasar Brazil. (Sport, via Metro)

Kocin Bournemouth Eddie Howe zai tattauna da manyan shugabannin kungiyar nan da awa 48, inda ake sa ran yanke hukunci kan makomarsa daga yanzu zuwa karshen makon nan. (Mail)

Bayern Munich ta amince ta yi £18.3m don dauko dan wasan Norwich City da Ingila da ke buga tamaula a rukunin 'yan kasa da shekara 21 Max Aarons, mai shekara 20. (Sky Sports)

Manchester City ta shirya don dauko dan wasan Wales da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Cameron Coxebayan Cardiff City ta saki dan wasan.(Wales Online)