Hotunan yadda Liverpool ta yi bikin lashe kofin Premier

Asalin hoton, @LFC
Liverpool ta yi bikin kofin da ta lashe na gasar Firimiya karon farko bayan shekaru 30
Liverpool ta karɓi kofin ne a gidanta Anfield bayan ta doke Chelsea 5-3.
Jordan Henderson - wanda ke jinya - shi ya karɓi kofin daga hannun tsohon fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Sir Kenny Dalglish a mumbari na musamman.
Jurgen Klopp ya kafa tarihi a Anfield inda karo na uku a kaka a jere ba a doke Liverpool ba a gidanta.
Tun saura wasa bakwai a ƙarƙare gasar Firimiya, Liverpool ta lashe kofin kuma yanzu wasa ɗaya ya rage inda za ta kai wa Newcastle ziyara ranar Lahadi.
Liverpool yanzu ta bar Chelsea da neman maki ɗaya a wasan ranar ƙarshe da za ta karɓi bakuncin Wolves domin samun shiga jerin ƙungiyoyi huɗun saman tebur ba da zai ba ta damar buga gasar zakarun turai ta Champions League.
Duk da cewa Liverpool ta yi bikin lashe kofinta ba tare da magoya baya ba a fili saboda annobar korona, amma bai hana wa magoya bayanta mamaye harabar Anfield ba.
Sai da ƴan sanda suka tarwatsa magoya bayan Liverpool a Anfield waɗanda suka dinga wasan wuta domin murnar nasarar ta lashe kofi bayan shafe shekaru 30.
Ga yadda Liverpool ta yi bikin lashe kofin

Asalin hoton, @LFC

Asalin hoton, @andrewrobertso5

Asalin hoton, @LFC

Asalin hoton, @LFC

Asalin hoton, @LFC

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, PA Media

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, AFP/Getty











