Chelsea na son ɗauko Henderson, Arsenal na da ƙwarin gwiwa kan Aubameyang

Dean Henderson

Asalin hoton, AFP

Chelsea ta shirya bai wa golan Ingila Dean Henderson £170,000 duk mako a yunkurin da take yi na dauko dan wasan mai shekara 23, wanda ke zaman aro a Sheffield United, domin ya bar Manchester United. (Manchester Evening News)

Henderson zai sake tafiya zaman aro har sai ya samu tabbaci daga Manchester United cewa za a ba shi damar fafatawa da golan Sufaniya David de Gea, mai shekara 29, wanda shi ne zabin farko na kungiyar. (Times - subscription required)

KazalikaChelsea za ta yi yunkurin dauko golan Barcelona da Jamus Germany Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 28, kuma ta shirya bayar da dan wasan Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, a wani bangare na yarjejeniyar. (Mundo Deportivo, via Mail)

KocinArsenal Mikel Arteta yana da "kwarin gwiwa" cewa dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, zai sabunta zamansa a kungiyar. (Independent)

Mutumin da ya mallaki Leeds United Andrea Radrizzani ya ce "za mu ga yadda za a yi" a kan yiwuwar dauko dan wasan Uruguay mai shekara 33 Edinson Cavani bayan kungiyar ta samu ci gaba a gasar Firimiya. Cavani ya bar Paris St-Germain a bazarar nan bayan kwangilarsa ta kare. (Sky Sports Italia, via Football Italia)

Za a ci gaba da rike kocin Newcastle United Steve Bruce idan Henry Mauriss, wanda ke gogayya da kamfanin Saudiyya a yunkurin sayen kungiyar, ya yi nasarar mallakarta. (Telegraph - subscription required)

Mai yiwuwa dan wasanAston Villa daTanzania Mbwana Samatta, mai shekara 27, zai kama gabansa zuwa Fenerbahce bayan ya gaza taka rawar gani tun da ya koma Villa Park a watan Janairu. (Takvim via Sport Witness)

Everton na sha'awar dauko dan wasan Southampton dan kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, amma ya shaida wa kungiyar cewa ya gwammace tafiya Tottenham. (Liverpool Echo)

GolanParis St-Germain Alphonse Areola, mai shekara 27, wanda ke zaman aro a Real Madrid, yana iya kama hanyarsa ta tafiya kungiyar da ke Ingila bayan iyalan dan wasan na Faransa sun sayi gida a London. (Marca)