Arsenal ta doke Man City 2-0 don kai wa zagayen ƙarshe na Cin Kofin FA

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Phil McNulty
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football writer at Wembley
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya yi wa mai gidansa Pep Guardiola zarra yayin da ƙungiyarsa ta kai zagayen ƙarshe na Gasar cin Kofin FA da nasarar da ta samu a Wembley.
Arteta, wanda ya bar aikinsa na mataimakin kocin Manchester City ya je ya gaji Unai Emery a Arsenal cikin watan Disamba, yanzu dai ya samu wata dama da zai iya yi wani abin a-zo-a-gani cikin kakarsa ta farko.
Yanzu dai zai tafi cike da taƙama don fuskantar ƙungiyar Chelsea ko Manchester United a karawar ƙarshe ranar 1 ga watan Agusta.
Gwarzon wasan Pierre-Emerick Aubameyang, zakaran duniya ɗan gaban Arsenal na faɗi tashi don cimma sabuwar kwanturagi ta dogon lokaci,, daidai lokacin da ya fito gazawar matakan baya na Man city.
Aubameyang dai ya zunduma ƙwallo kai tsaye a ragar Ederson da ƙwaƙƙwarar dama ɗaya da ya samu amma ƙaddara ta riga fata ga City bayan minti na 19 lokacin da ya nuna gagarumar fasaha wajen isar da ƙwallon da Nicolas Pepe ya kwaso.
City dai ta mamaye wasan bayan an dawo daga hutu amma suka yi ta ɓarar da damammaki har sai da Aubameyang ya sake koya musu darasi a minti na 71 lokacin da ya janyo ƙwallo daga gefen tsakiyar fili kuma ya watsa ta ta ƙasan gola.







