Salah ba shi da tabbaci na ci gaba da zama a Liverpool, Manchester United na son ɗauko Oblak

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Liverpool Mohamed Salah, mai shekara 28, ya ce "babu wanda ya san makomata ko kuma abin da zai faru da ni nan gaba" lokacin da aka tambaye shi a kan makomarsa a kungiyar. (La FM Colombia - video)
Manchester United na sanya ido kan golan Atletico Madrid da Slovenia wanda za a sayar kan £109m, Jan Oblak, mai shekara 27, a matsayin dan wasan da zai maye gurbin golan Sufaniya David de Gea. (Sun)
Crystal Palace ta gaya wa dan wasan Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 27, cewa zai iya barin Selhurst Park idan aka taya shi da daraja, wato kamar £40m. (Times - subscription required)
Arsenal, West Ham da kuma Everton suna son karbo aron dan wasan Barcelona wanda ya taimaka wa Faransa ta lashe Kofin Duniya Samuel Umtiti, mai shekara 26. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Brighton ta taya dan wasan Jamus da ke buga tamaula a rukunin 'yan kasa da shekara 21 Luca Kilian, mai shekara 20, don dauko shi daga Paderborn a kan £3m. (Mail)
Benevento na sha'awar dauko tsohon dan wasan Liverpool da Ingila Daniel Sturridge, mai shekara 30, idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo. (Mail)
Manchester United na fuskantar yin asarar £70m yayin da Chelsea ke fuskantar rasa £50m idan suka gaza shiga cikin 'yan hudun saman teburin Firimiya har aka kammala kakar wasan bana sannan suka kasa samun gurbi a gasar Zakarun Turai mai zuwa. (Sun)







