Arsenal za ta bai wa Aubameyang kwangila mai romo, Gerrard ya ƙi zama kocin Bristol City

Arsenal striker Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, EPA

Arsenal ta shirya sabunta kwangilar dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, inda zai rika karbar £250,000 duk mako tare da karin alawus-alawus, a yunkurin da take yi na rarrashinsa ya ci gaba da zama. (Telegraph)

Borussia Dortmund na son dauko dan wasanWerder Bremen dan kasar Kosovo Milot Rashica, mai shekara 20, a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho, wanda ake sa ran zai tafi Manchester United. (Telegraph)

KocinRangers Steven Gerrard, mai shekara 40, ya ki amincewa da tayin da aka yi masa na zama sabon kocin Bristol City.(Bristol Post)

Valencia na shirin zawarcin dan wasan Chelsea da Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, da kuma dan wasanManchester City David Silva, mai shekara 34. (90min)

Dan wasan Bayern Munich Leroy Sane, mai shekara 24, ya shawarci dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 28, ya ci gaba da zama a kungiyar maimakon tafiya tsohuwar kungiyarsa Manchester City, ko kuma Real Madrid. (Sport Bild, via Independent)

Tottenham na da kwarin gwiwa kan dauko dan wasan Southampton da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, ko da yake an amince da tayin Everton na sayensa kan £25m. (Guardian)

Dan wasan Ingila Japhet Tanganga, mai shekara 21, ya kusa komawa Tottenham. (Evening Standard)

WatakilaBayer Leverkusen ta nemi karbo aron dan wasan Real Madrid dan kasar Brazil Reinier, da shekara 18, idan dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, ya tafi Chelsea. (Goal)

Arsenal na duba yiwuwar dauko dan wasan Aston Villa Douglas Luiz, mai shekara 22, amma Manchester City za ta iya tsauwala kudi kan dan wasan na Brazil. (90min)

Porto ta ware £6.3m don dauko dan wasan Portugal Ruben Semedo, mai shekara 26, daga Olympiakos. (Sport 24 - in Greek).