Newcastle za ta dauko McGinn, Chelsea na zawarcin Tagliafico

John McGinn

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Newcastle Steve Bruce na shirin dauko dan wasan tsakiyar Scotland John McGinn, mai shekara 25, a bazara idan aka fitar Aston Villa daga gasar Firimiya. (Star)

Kocin Southampton Ralph Hasenhuttl ya shaida wa Tottenham cewa akwai bukatar ta yi tayi mai kyau kan dan wasan Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24 bayan Everton ta ce za ta saye shi a kan £25m. (Evening Standard)

Leicester da Newcastle sun bi sahun kungiyoyin da ke son dauko dan wasan Norwich dan kasar Ingila Todd Cantwell. (Mail)

Chelsea da Atletico Madrid suna sanya ido kan dan wasan Ajax da Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, wanda ake rade radin zai tafi Manchester City. (Sun)

Manchester City ta dage a yunkurinta na dauko dan wasan Valencia Ferran Torres amma ta gaya wa kungiyar ta Sufaniya cewa ba za ta iya biyan euro 35m kan dan wasan mai shekara 20 ba. (Marca)

Kocin Tottenham Jose Mourinho ya yi amannar cewa dan wasan Ingila dan shekara 19 Oliver Skipp, wanda ya sanya hannu kan sabon kwantaragi a kungiyar, nan gaba zai zama kyaftin din Tottenhan. Skipp yana son tafiya zaman aro domin ya samu kwarewa amma Mourinho ya fi so ya zauna a kungiyar. (Evening Standard)

Tottenham sun kusa kammala sayen dan wasan Wigan dan shekara 15 Alfie Devine. (Mail)

Manchester United za ta ba da dama ga dan wasan Netherlands Timothy Fosu-Mensah, mai shekara 22, ya yi dogon zama a kungiyar a yayin da wasu kungiyoyin Jamus ke son daukarsa. (Manchester Evening News)

Tsohon golan Sufaniya Iker Casillas, mai shekara 39, zai koma Real Madrid a matsayin mai bayar da shawara, shekara biyar bayan ya bar kungiyar inda ya tafi Porto. (Marca)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce yana son dan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 29, ya zauna a kungiyar. (Evening Standard)

Idan Lacazette ko dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31, suka bar kungiyar a bazara, Arsenal za ta iya dauko dan wasan Celtic dan kasar Faransa Odsonne Edouard, mai shekara 22. (Bleacher Report)

Kocin Barcelona Quique Setien ya amince cewa ba shi da tabbacin ci gaba da zama a kungiyar zuwa watan gobe don fafatawa da Napoli a ci gaba da wasan Zakarun Turai.