Fifa ta ce za a iya ci gaba da canja 'yan wasa biyar zuwa Agustan 2021

Gabriel Jesus and Sergio Aguero

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gasar Premier League za ta iya ci gaba da tsarin sauya 'yan kwallo biyar bayan da Fifa ta amince da hakan

An bai wa kungiyoyi damar ci gaba da tsarin sauya 'yan wasa biyar a lokacin tamaula zuwa karshen kakar 2020-21, bayan da Fifa ta amince da tsawaita hukuncin.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce zabi ya ragewa kasashe da masu tsara wasanni idan sun amince su ci gaba da sauya 'yan kwallo biyar din ba dole.

Za a iya amfani da dokar zuwa Agustan 2021, hakan na nufin gasar cin kofin nahiyar Turai da ta Copa America za su iya amfana da tsarin.

Fifa ta ce ''Walwala da lafiyar 'yan wasa shi ne mafi mahimmaci da ya sa ta dauki wannan matakin.''

An amince da dokar sauya 'yan wasa biyar daga ukun da aka saba a tamaula ne a lokacin da ake kulle saboda cutar korona.

An kuma yi hakan ne don kare 'yan kwallo daga yin rauni ganain wasannin da za su dunga buga wa kusa da juna.

Premier League ta fara amfana da dotar ranar 17 ga watan Yuli lokacin da aka ci gaba da wasanni bana, bayan wata uku da aka dakatar da gasar saboda cutar korona.

Sai dai kuma dokar ta bayar da damar sau uku ne za a sauya 'yan wasa biyar don gudun ba ta lokaci a yayin da ake taka leda.

Hakan na nufin za a iya sauya dan wasa daya sai kuma a saka biyu daga karshe a sa uku a cikin fili.

Ko kuma a fara da sa uku, sai biyu sannan a karkare da daya, kar da ya wuce zuwa uku wajen sa 'yan wasa biyar a lokacin wasanni.