Pogba zai sabunta zamansa a Manchester United, sai karshen Agusta Havertz zai koma Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, 27, yana dab da amincewa da sabon kwantaragin shekara biyar a Manchester United. (Sun)
Bayer Leverkusen ta amince da matakin da dan wasan Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, ya dauka na komawa Chelsea amma tana so ta jinkirta tafiyarsa sai karshen watan Agusta. (Daily Star)
Manchester Cityna son dauko dan wasanAjax da Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27, a bazara. (Sports Illustrated)
Dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29, yana da kwarin gwiwar kammala tafiya Liverpool bayan ya ki amincewa ya sabunta kwangilarsa a Bayern Munich. (Daily Mirror)
Manchester United ta kulla yarjejeniya da dan wasan Real Madrid mai shekara 17 Alvaro Fernandez Carreras, wanda zai sanya hannu kan kwangilar shekara hudu a Old Trafford. (AS - in Spanish)
Tsohon kocin Southampton da Tottenham Mauricio Pochettino na cikin wadanda Inter Milan da Juventus suke son daukowa idan kungiyoyin na Italiya suka kori koci-kocinsu - Antonio Conte da Maurizio Sarri - a karshen kakar wasan bana. (Daily Telegraph)
Dole sai kocinInter Conte ya gamsar da hukumar gudanarwar kungiyar kafin a amince a kan albashin N'Golo Kante sannan a dauko dan wasa na Faransa mai shekara 29 daga Chelsea. (SempreInter)
Dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, dan shekara 17, ya kammala gwajin lafiyarsa a Borussia Dortmund gabanin tafiya kungiyar daga Birmingham ko da yake zai kammala kakar wasan bana a the Blues. (Sky Sports).
Dan wasan Algeria Yasser Larouci, dan shekara 19, ya shirya barin Liverpool a bazarar nan, inda aka ce Leeds da Brentford suna cikin kungiyoyin da ke zawarcinsa. (Goal.com)
Watakila Tottenham za ta karasa kakar wasan bana ba tare da dan wasan Ivory Coast Serge Aurier, mai shekara 27 ba, saboda ya tafi Faransa sakamakon mutuwar dan uwansa. (Evening Standard)
Everton ta taya dan wasanNapoli Allan, amma kungiyar ta Italiya tana jan kafa kan sayar da dan wasan na Brazil mai shekara 29. (Sport Witness)
Roy Hodgson ya ce sayen sabbin 'yan wasan da za su murza leda a Crystal Palace a bazara zai bai wa kungiyar damar kara himma a kakar wasan da ke tafe domin samun gurbin 'yan goman saman teburi. (Evening Standard)
Manchester City ta kulla yarjejeniya da dan wasan Valencia dan kasar Sufaniya Ferran Torres, mai shekara 20. (Eurosport)
West Ham, Norwich da kuma Watford suna son dauko dan wasan QPR dan kasar Jamhuriyar Ireland Ryan Manning, mai shekara 24. (Football Insider).











