Napoli ta rage farashin Koulibaly, Manchester City na son ɗauko Martinez

Kalidou Koulibaly

Asalin hoton, Getty Images

Napoli ta gaya waManchester City ta biya ta £65m don daukar dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, wanda ake rade-radin zai koma Liverpool ko Manchester United kuma a baya aka sanya £80m a kansa. (Daily Mirror)

Manchester City tana son dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, ya maye gurbin Sergio Aguero, mai shekara 32 a shirinta na tsawon lokaci. (Sky Sports)

Sai dai Martinez yana dab da kammala yarjejeniya da Barcelona. (Marca)

Bayern Munich tana son karbar euro 40m kan tsohon dan wasanBarcelona Thiago Alcantara, dan shekara 29 wanda ake hasashen zai koma Liverpool. (Sport Bild, via Daily Mirror)

Ana tunanin Bayern ta fasa shirinta na dauko dan wasan da Chelsea take zawarci Kai Havertz, wato dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus mai shekara 21. (Sport Bild, via Daily Mail)

Ana sa ranEverton, Atletico Madrid da kumaBayern Munich za su fafata wajen zawarcin dan wasan Crystal Palace da Ivory Coast Wilfried Zaha a bazarar nan, inda ita ma Newcastle take kokarin dauko dan wasan mai shekara 27. (Daily Mail)

Southampton na fatan kulla yarjejeniyar dindindin ta £10m kan dan wasan Tottenham dan kasar Ingila Kyle Walker-Peters, mai shekara 23, wanda yake zaman aro a Saints tun watan Janairu. (Sun)

Kocin Southampton Ralph Hasenhuttl ya ki amincewa ya tattauna yiwuwar musaya tsakanin dan wasan Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, wanda ke son tafiya Tottenham, da kuma Walker-Peters. (Sky Sports)

Dan wasan Birmingham dan shekara 17 Jude Bellingham ya amince da yarjejeniyar £22.5m don tafiya Borussia Dortmund. (Bild)

Rahotanni sun ce dan wasan Ghana Thomas Partey, mai shekara 27, ba zai amsa tayin tafiya Arsenal ba kuma zai sanya hannu kan sabon kwantaragi a Atletico Madrid, wacce ta amince ta ninka albashinsa. (GhanaSoccerNet, via Daily Mail)

Pep Guardiola yana son dauko dan wasan Aston Villa dan kasar Brazil Douglas Luiz, mai shekara 22, domin dawo da shi Manchester City idan aka bude kasuwar 'yan kwallo a watan nan na Yuli. (Birmingham Mail)

Dan wasan Liverpool Adam Lallana, mai shekara 32, wanda ke shirin barin kungiyar a bazarar nan, ya samu goyon gayyata daga wurinr Leicester, Burnley da kuma Brighton. (Daily Star)

Dan wasan Tottenham dan kasar Ingila Danny Rose yana fatan zai sauya zaman aron da yake yi a Newcastle zuwa na dindindin. (Newcastle Chronicle).