Chelsea za ta biya euro 100m kan Oblak, PSG na son ɗauko Marcus Rashford.

Jan Oblak

Asalin hoton, EPA

Chelsea ta amince ta biya euro 100m domin dauko golan Atletico Madrid dan kasar Slovenia Jan Oblak, mai shekara 27. (AS - in Spanish)

Paris St-Germain ta mayar da dauko dan wasan Manchester United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 22, a matsayin babban abin da ta sanya a gaba. (Independent)

Barcelona ta amince ta ba da dan wasanBrazil Philippe Coutinho, mai shekara 28, ga Arsenal ko Newcastle a yayin da take neman kudin dauko dan wasan Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22. (Goal)

Dan wasan Brazil Neymar, mai shekara 28, yana so ya koma Barcelona, kuma tuni Paris St-Germain ta soma auna darajarsa ganin cewa saura shekara biyu ya kammala kwangilarsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan Southampton da Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, yana son tafiya Tottenham, wacce za ta sanya dan wasan Ingila Kyle Walker-Peters, mai shekara 23, a cikin yarjejeniyar. (Evening Standard)

Dan wasanLille da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 21, ya zabi tafiya Napoli a wata yarjrjeniya da ta kai euro 81m. (RMC Sport - in French)

Manchester United ba za ta cika alkawarinbiyan £25m ga kamfanin Adidas da ke yin kayan wasa ba idan ta gaza samun gurbin gasar Zakarun Turai ta kakar wasa mai zuwa. (Daily Mail)

Sporting Lisbon na sha'awar karbo aron dan wasan Manchester City dan shekara 20 Pedro Porro. (A Bola - in Portuguese)

Barcelona ta yi amfani da damar dauko dan wasan Sao Paulo dan shekara 19 Gustavo Maia. (ESPN)

Everton tana tattaunawa da FC Twente game da sha'awar da kungiyar ta Netherlands ke yi ta dauko Nathangelo Markelo, mai shekara 21, don komawa da shi gida a matsayin aro. (Liverpool Echo)