Shin ko Lionel Messi na bukatar hutu ne a Barcelona?

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Kyaftin din Barcelona Lionel Messi na fatan kungiyarsa za ta kare kofin La Liga da ta lashe a bara, sai dai kuma kwazonsa ya ragu a wasanni da yake yi.

Kwallo uku kyaftin din tawagar Argentina ya ci wa Barcelona tun da aka ci gaba da gasar La Liga ta bana, wacce aka dakatar cikin watan Maris, saboda cutar korona.

Cikin watan Yuni aka koma fafatawar La Liga, inda Messi ya zura kwallo uku a raga a gasar da tun bayan da aka ci gaba da wasannin, kuma biyu fenariti ya ci.

Ba wai rashin cin kwallo ne za ka fahimci Messi na bukatar hutu ba, ya rage kazar-kazar da yanka da kuma guje-guje da ya saba a lokacin da yake yi wa Barca wasanni.

Barcelona ta doke Villareal da ci 1-0 ranar Asabar a wasan mako na 36, kuma Arturo Vidal ne ya ci kwallon bayan da Messi ya tura masa fasin.

Hakan ne ya sa kyaftin din Barcelona, ya bayar da kwallo 20 aka kuma zura su a raga a kakar tamaula ta bana shi ne kan gaba a lissafi.

Kawo yanzu Messi ya zura kwallo 22 a raga a gasar La Liga ta wannan shekarar, mai biye da shi Karim Benzema na Real Madrid yana da 18.

Dan wasan Villareal, Gerard Morenoya ci kwallo 16 a kakar bana, kuma shi ne na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar.

Tun kan a dakatar da wasannin La Liga saboda cutar korona, Barca ce ta daya a kan teburi daga baya Real ta karbe ragama, bayan da ta lashe wasannin da ta buga tun daga Yuni kawo yanzu.

Rabon da Real Madrid ta lashe kofin La Liga tun kakar 2016-17, yayin da Barcelona ce ke rike da biyu a jere da ta dauka a 2017-18 da 2018-19.

Real Madrid za ta ziyarci Manchester City a wasa na biyu na Champions League ranar 7 ko kuma 8 ga watan Agusta.

Wasan farko da suka buga a zagayen kungiyoyi 16 da ke gasar Zakarun Turai a Spaniya, City ce ta yi nasara da ci 2-1.

Ranar Litinin Real Madrid za ta ziyarci Granada a wasan mako na 36, kuma a fafatawar farko da suka yi ranar 5 ga watan Oktoban 2019, Real ce ta yi nasara da ci 4-2.

Wadan da suka ci mata kwallayen sun hada da Karim Benzema da Eden Hazard da Luka Modric da kuma James Rodriguez.

Ita kuwa Granada ta zare kwallon farko a bugun fenariti ta hannun Darwin Machis, sannan Domingos Duarte ya ci mata na biyun.