Fati zai kafa tarihin cin kwallo a matsayin matashi a Spaniya

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona mai rike da La Liga na bara na ta kokarin yadda za ta kare kofinta a bana, shi kuwa Ansu Fati na fatan kafa tarihi a gasar ta Spaniya.

Matashin dan wasan Barcelona, Fati na shirin karya tarihin cin kwallo a matsayin matashi mai shekara 17 a gasar ta Spaniya.

Kawo yanzu matashin ya ci kwallo shida a gasar La Liga, inda ya fara zura wa a karawa da Osasuna a lokacin yana da shekara 16 da haihuwa.

Hakan ne ya sa Fati ya doke tarihin da Bojan Krkic ya kafa a matakin matashin da ya zura kwallo a raga a gasar ta Spaniya.

Fati shi ne matashin da ya ci kwallo a gasar Champions League yana da shekara 17 da kwana 40 a fafatawa da Inter Milan.

Kawo yanzu Pablo Quintana ya ci kwallo 11 a kakar 1933/34 kafin ya cika shekara 18 shi ne a kan gaba a tarihi.

Ansu Fati yana da damar karya wannan tarihin kafin ya kai shekara 18 ranar 31 ga watan Oktoban 2020.

Wadanda suka kusan doke tarihin da Pablo ya kafa sun hada da Bojan daga La Masia wanda ya ci kwallo 10 a raga a 2007/08 kan ya kai shekara 18.

Sai kuma Raul Gonzalez na Real Madrid da ya zura kwallo tara a babbar kungiyar a 1994/95 a gasar ta La Liga.

Ansu Fati na jiran Barcelona ta gabatar masa da kunshin kwantiragi mai tsoka da zai ci gaba da buga mata tamaula da ya fara tun daga makarantar kungiyar.