Guardiola ya ce Man City za ta yi wa Liverpool tarbar girma

Manchester City players walk out to a guard of honour

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dethroned champions Manchester City have been the recipients of a guard of honour on several occasions

Pep Guardiola ya ce 'yan wasan Manchester City za su yi wa na Liverpool wacce ta lashe kofin Premier League tarbar girma idan za su kara a Etihad ranar Alhamis.

Shi ne wasan farko da Liverpool za ta buga a Premier League, tun bayan da ta lashe kofin a karon farko tun bayan shekara 30.

Liverpool ta ci kofin bana saura wasa bakwai-bakawi a karkare kakar bana da tazarar maki 23 tsakaninta da Manchester City.

Kuma nasarar da Chelsea ta doke Manchester City da ci 2-1 a gasar Premier League a Stamford Bridge ya sa kungiyar ta Anfield ta zama zakara a shekarar nan.

"Za mu yi wa Liverpool tarbar girma da zarar sun zo Etihad buga wasan Premier League," in ji kocin City, Guardiola.

"Za mu gaisa da Liverpool da zarar sun zo gidanmu kuma ta kayatatciyar hanya, Za mu yi haka ne ba don komai ba don sun cancanta."

Sai dai kuma Guardiola bai ce komai ba kan tambayar da aka yi masa ko zai tsawaita zamansa a City, bayan da yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar 2021.

A lokacin zai cika shekara biyar yana jan ragamar Manchester City, fiye da shekarun da ya yi a Barcelona.

Tuni ake cewa Guardiola na son gwada sa'a a wata kungiyar, musammam idan aka tabbatar da hukuncin dakatar da kungiyar kaka biyu daga shiga gasar Zakarun Turai.