Maradona na son dauko Ronaldinho, Arsenal na son Partey

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya kasa ba dan wasansa Matteo Guendouzi tabbacin cewa zai bar kulub din a karshen kaka bayan dan wasan tsakiyar na Faransa ya nuna yana son barin kungiyar. (Guardian)
Manchester United ta shiga sahun manyan kunhiyoyin da ke neman Guendouzi, kamar yadda Barcelonada Paris St-Germainda Inter Milan da kuma Atletico Madrid dukkaninsu suka nuna sha'awar dan wasan na tsakiya. (L'Equipe, via Mail)
Celtic na tunanin dauko Joe Hart, mai shekara 33, bayan Burnley, ta rabu da shi idan kuma har kungiyar ta Scotland ta kasa samun dauko aron golan Ingila Fraser Forster, mai shekara 32, daga Southampton. (Telegraph)
Arsenal na sanya ido kan dan wasan tsakiya Danilo Pereira, inda Porto ta nuna za ta karbi fam miliyan 20 kan dan wasan mai shekara 28, yayin da kuma Arsenal ta ke son dauko dan wasan Atletico Madridda Ghana Thomas Partey, mai shekara 27. (ESPN)
Inter Milan na dab da dauko dan wasan Real Madridna Morocco Achraf Hakimi, mai shekara 21, wanda Borussia Dortmund, ta karba aro. (Guardian)
Dan wasan daArsenal take so Layvin Kurzawa, mai shekara 27, yana dab da sanya hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da Paris St-Germain idan kwangilar shi ta kawo karshe 30 Yuni. (RMC Sport, via Sun)
Dan wasan tsakiya naBirmingham Jude Bellingham, da ake alakanta wa da Manchester United da Borussia Dortmund, ana tunanin zai sanya hannu kar yarjejeniya idan ya kai shekara 17 a ranar Litinin amma har yanzu bai shaida wa kocin kungiyarsa ba Pep Clotet game da makomarsa. (Mirror)
Ana tunanindan wasan aro naArsenal Dani Ceballos zai koma kungiyarsa ta farko Real Betis idan dan wasan na Sifaniya mai shekara, 23, ya koma Real Madrid a karshen kaka. (Marca)
Kocin Gimnasia y Esgrima La Plata Diego Maradona yana fatan dauko tsohon dan wasan Brazil Ronaldinho, mai shekara 40, daga ritaya don ya bugawa kungiyarsa da yake horar wa ta Argentina. (Marca)
Dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 19, ba ya tunanin barin Borussia Dortmund, duk da ana alakanta shi da Real Madrid da Manchester United. (Westdeutsche Allgemeine Zeitung - in German)
Tottenham ta yi wa Maurizio Pochettino, mai shekara 19, tayin sabuwar yarjejeniya wanda dan tsohon kocin kungiyar ne Mauricio. (Standard)











