Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Za a bude filayen wasan kwallon kafa a Faransa ga magoya baya 5,000
Za a fara barin magoya bayan wasanni a Faransa su rika shiga kallo daga 11 ga watan Yuli, in ji gwamnatin kasar, a kokarin da take na sassauta dokar kullen da aka kakaba saboda korona.
Amma za a bar mutum 5,000 ne kawai su rika shiga kallon da farko, kuma ana sa ran za a kara adadin daga baya.
"Za a kara fitar da wasu sabbin hanyoyin shawo kan cutar nan da tsakiyar watan Yuni tare da duba yiyuwar kara sassautawa a karo na biyu cikin Agusta," in ji gwamnatin.
Wannan sanarwar na nufin za a ci gaba da buga wasannin French Cup da League Cup a gaban masoya kwallo - duka gasar biyu an dakatar da su ne sakamakon annobar korona.
An soke gasar French League ne a watan Afirilu, kuma yadda jerin jadawalin kungiyoyin yake haka aka tsayar da shi.
PSG da ke saman tebirin da tazarar maki 12 kan tsayar da gasar ce aka bayyana a matsayin wacce ta lashe gasar, yayin da Amiens da Toulouse aka bayyana su a matsayin wadanda suka fada rukuni na biyu na gasar.