Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Paul Pogba: Kocin Man Utd Ole Gunnar Solskjaer yana so ɗan wasan ya nuna jagoranci a filin wasa
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer yana so ya ga Paul Pogba yana shugabanci a filin wasa.
Sau biyu kawai dan wasan mai shekara 27 ya buga wa kungiyar wasa tun daga watan Satumba saboda karayar da ya yi a kafa.
Kuma duk da rade-radin da ake yi kan rashin tabbacin makomarsa a kungiyar, damar da Pogba yake da ita ta ci gaba da zama a United ta karu - inda ake sa ran kasuwar musayar 'yan kwallon kafa za ta rushe saboda tasirin annobar Covid-19 kan harkokin kudin kungiyoyi.
Solskjaer ya ce: "Paul yana daya daga cikin kwararrun 'yan wasan tsakiya na duniya."
"Ya jagoranci lashe Kofin Duniya kuma ina son irin wannan shugabanci a filin wasa."
Pogba bai sake buga wa United wasa ba tun ranar 26 ga watan Disamba a yayin da yake kokarin komawa ganiyarsa bayan jinyar da ya yi, amma ya fuskanci koma-baya wanda ya sanya aka yi tiyata a kafarsa a watan Janairu.
A yayin da United za ta koma Gasar Firimiya a fafatawarda za ta yi da Tottenham ranar Juma'a - wata fiye da uku bayan an dakatar da gasar sanadin annobar korona - Solskjaer yana so dan wasan Faransa ya taka muhimmiyar rawa.
"Da yake yanzu ya komo kan ganiyarsa kuma zai iya buga wasa, na ga yadda lafiyarsa take, kuma a shirye yake ya sake murza leda," in ji Solskjaer.
"Ban sani ba ko zai yi miniti 45 ko 60 yana murza leda amma na san cewa a hankali zai warware, kuma muna fata nan da watanni kadan masu zuwa zai koma kamar yadda yake a baya."
BBC Sport ta fahimci cewa masu horaswa na United sun samu kwarin gwiwa yadda Pogba da Bruno Fernandes wanda aka dauko a watan Janairu suka shiga tawagar da ta buga wasan sada zumunci makon jiya inda West Brom ta doke ta a Old Trafford.