Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Man Utd Marcus Rashford da Paul Pogba sun shirya komawa tamaula
'Yan wasan Manchester United biyu Marcus Rashford da Paul Pogba za su kasance cikin wadanda za a zaba domin buga tamaula idan aka komo Gasar Premier, a cewar kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer.
Rashford da Pogba sun yi doguwar jinya lokacin da aka dakatar da gasar saboda annobar korona a watan Maris.
Dukkan 'yan wasan sun koma atisaye na rukunin wasu 'yan wasa marasa yawa inda suka hadu da sauran 'yan wasan United a makon jiya.
Solskjaer ya ce: "Sun ['yan wasan biyu] warke sosai."
"Sun bi sahun masu yin atisaye yanzu kuma sun yi duk abin da sauran 'yan wasan suke yi. Ya zuwa yanzu babu wata matsala da suka fuskanta.
"Idan muka koma buga gasa, za mu samu cikakkiyar tawaga inda za mu zabi wanda muke so."
Rashford ya yi fama da ciwon baya tun watan Janairu yayin da Pogba bai buga galibin wasannin da United ta fafata a cikinsu ba na kakar wasa ta bana saboda ciwon kafa.