Marcus Rashford zai yi jinya

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer na sa ran Marcus Rashford zai yi jinyar makonni.

Dan wasan tawagar Ingila ya ji rauni ne a wasan FA Cup da United ta ci Wolverhampton 1-0 ranar Laraba.

Rashford bai buga wasan Premier na mako na 23 da Liverpool ta doke United da ci 2-0 ranar Lahadi a Anfield ba.

Rashford ya ci kwallo 22 a United da tawagar Ingila a bana, inda ya zura 14 a raga a gasar Premier.

United ta ci gaba da zama a mataki na biyar a kan teburi, bayan buga wasa 23 tana da maki 34.

A ranar Laraba ne United za ta karbi bakuncin Burnley a wasan mako na 24.