Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a kammala Champions da Europa League cikin watan Agusta
Za a karkare gasar Zakarun Turai ta bana ta Champions da ta Europa League da kungiyoyi takwas-takwas a Lisborn din Portugal da wasu a biranen Jamus cikin Agusta.
Ita ma gasar Champions League ta mata za a yi ta siri daya kwale a Arewacin Spaniya tsakanin 21 zuwa 30 ga watan Agusta.
An dakatar da wasannin cin kofin Zakarun Turai a cikin watan Maris saboda bullar cutar korona.
Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, Uefa ta ce dukkan birane 12 da tun farko aka amince da su to za su karbi bakuncin wasannin Euro 2020 a badi.
Za a gudanar da Euro 2020 daga 11 ga watan Yunin 2021. Za kuma a buga wasannin cike gurbi daga 8 ga watan Oktoba da 12 ga watan Nuwamba.
Za a ci gaba da Champions League wasannin zagaye na biyu da suka rage na kungiyoyi da za a yi ranar 7 da 8 ga watan Agusta.
Wasannin zagaye na biyun da aka dakatar sun hada da Manchester City da Real Madrid da Chelsea da Bayern Munich, Juventus da Lyon da na Napoli da Barcelona.
Wadannan wasannin ne Uefa ta ce ba ta fayyace ko kungiyoyin za su buga karawar a filayensu ko kuma su fafata a filin da bana kowa ba.
Daga nan ne za a shiga karawar gaba a Lisborn daga 12 zuwa 13 ga watan Agusta, sannan a buga wasan karshe ranar 23 ga watan Agusta a Portugal.
Tun farko birnin Istanbul aka tsara zai karbi bakuncin wasan karshe na kakar 2020 yanzu an amince zai yi a 2021.
Za a ci gaba da wasannin Europa League daga 10 ga watan Agusta. Za a yi sauran wasannin da suka rage na kungiyoyi 16 daga 5 zuwa 6 ga watan Agusta.
A wasannin mata kuwa tuni Arsenal da Glasgow City suka kai karawar daf da na kusa da na karshe da za su ci gaba da wasanni a birnin Bilbao Bilbao da San Sebastian tsakanin 21 zuwa 30 ga Agusta.
Za a karkare a wasan karshe a birnin San Sebastian ranar 30 ga watan Agusta.