Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zan so Bayern ta lashe Champions League na bana — Berbatov
Dimitar Berbatov ya ce yana son yaga Bayern Munich ta lashe kofin zakarun Turai na Champions League na bana na kuma shida a tarihi.
Tsohon dan wasan Tottenham da Manchester United ya ce Bayern ce keda damar daukar kofin bana, da zarar an ci gaba da gasar shekarar nan.
Bayern ta doke Chelsea a Ingila a wasannin kungiyoyi 16 da suka rage a gasar karawar zagayen farko, daga baya aka dakatar da gasar saboda bullar cutar korona.
Berbatov ya ce yadda yaga Bayern ta ragargaji Chelsea a wasan farko da 'yan kwallon da take da su yaga ya kamata kungiyar ta Jamus ta zama zakara a kakar 2019-20.
Berbatov, mai shekara 39 wanda ke kan gaba a ci wa kasarsa Bulgaria kwallo a tarihi da 48 wanda ya taka leda a Tottenham da Manchester United, ya kuma yi wasa a Fulham da Bayern Leverkusen da kuma Monaco.
Dan wasan ya kara da cewar Bayern tana da dama fiye da kowacce kungiyar Turai a bana, bayan da take buga gasar Bundesliga kawo yanzu, kuma tana taka rawar gani tun lokacin da aka ci gaba da wasannin bana cikin watan Mayu.
Bayern Munich na shirin lashe kofin Bundesliga na 50 a tarihi, bayan da ta doke Fortuna Duesseldorf da ci 5-0 ranar Asabar a wasannin mako na 29.