Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Adam Lallana ya saka hannu kan 'yar gajeriyar yarjejeniya a Liverpool
Adam Lallana ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Liverpool zuwa karshen kakar bana.
Dan kwallon tawagar Ingila mai shekara 32 zai bar Liverpool a karshen watan Yuni a lokacin da kwantiraginsa ya cika.
Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da gasar Premier ta 2019-20, bayan kwana 100 da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.
Liverpool tana ta daya a kan teburin Premier na bana da tazarar maki 25 ta kuma daf da lashe kofin gasar na farko tun bayan shekara 30.
Wasan farko da Liverpool za ta yi idan an ci gaba da wasannin shi ne da Everton ranar 21 ga watan Yuni ta buga na karshe a kakar bana ranar 26 ga watan Yuni da Newcastle United.
Lallana ya yi fama da jinya a kaka biyu da ta wuce ya kuma buga wa Liverpool wasa 15 a bana ya ci mata kwallo daya tal.
Ya kuma koma Anfield daga Southampton kan fam miliyan 25 a shekarar 2014 lokacin Bendan Rodgers wanda ake cewa zai kai shi Leicester City a yanzu haka.