Newcastle 'za ta sayo Coutinho da Shaqiri, Arsenal da Tottenham na son dauko Willian'

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta soma tattaunawa don dauko dan wasan Barcelona Philippe Coutinho, mai shekara 28, bayan Bayern Munich ta janye daga wajen dan wasan na Brazil a mataki na dindindin. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Kazalika Newcastle ta ce za ta dauko dan wasan Liverpool Xherdan Shaqiri, dan shekara 28, idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa. Sau 10 kawai dan wasan na Switzerland ya buga kwallo a Liverpool a kakar wasa ta bana. (Mail)
Tana ƙasa tana dabo game da £300m da Saudiyya ta ware domin sayen Newcastle saboda Hukumar Cinikayya ta Duniya ta ce kasar ce ta dauki nauyin wani shirin talabijin da ke satar fasaha sannan ya watsa labaran wasanni ta hanyar intanet ba tare da bin ƙa'ida ba. (Guardian)
Arsenal da Tottenham suna gogayya wajen ganin sun dauko dan wasan Chelsea da Brazil Willian, mai shekara 31, wanda kwangilarsa za ta kare a Stamford Bridge a bazarar da muke ciki. (Telegraph)
Wolves za ta soma zawarcin dan wasan Sporting Lisbon dan kasarPortugal Joao Palhinha, mai shekara 24, wanda za a sayar a kan £18m. (Mirror)
Manchester City tana kan gaba a yunkurin dauko dan wasan Ajax Sontje Hansen, dan shekara 18, wanda ya lashe kyautar Golden Boot ta Kofin Duniya na 'yan kasa da shekara 17 a bazarar da ta wuce. (Goal)
Vitoria Guimaraes tana son sayo dan wasan Crystal Palace Jadan Raymond, dan shekara 16, a kan £250,000 a yayin da kwangilarsa take shirin karewa watan gobe. (Sky Sports)







