Odion Ighalo: Man Utd 'tana tattaunawa' kan tsawaita zaman dan wasan

Odion Ighalo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ighalo ya zura kwallo hudu a wasa takwas da ya buga wa Manchester United

Manchester United tana "tattaunawa" da Shanghai Shenhua da zummar tsawaita zaman dan wasan da ta karbo aro Odion Ighalo, a cewar koci Ole Gunnar Solskjaer.

United ta karbi aron Ighalo, mai shekara 30, a watan Janairu kuma zai China ranar 31 ga watan Mayu idan ba a cimma yarjejeniyar da za ta kai ga tsawaita zamansa zuwakarshen kakar wasa ta bana ba.

Solskjaer ya shaida wa MUTV cewa "A halin da ake ciki ba a cimma matsaya ba."

A bangare daya, Ole Gunnar Solskjaer ya ce Marcus Rashford da Paul Pogba za su kasance cikin wadanda za a zaba domin buga tamaula idan aka komo Gasar Premier.

Rashford da Pogba sun yi doguwar jinya lokacin da aka dakatar da gasar saboda annobar korona a watan Maris.

Dukkan 'yan wasan sun koma atisaye na rukunin wasu 'yan wasa marasa yawa inda suka hadu da sauran 'yan wasan United a makon jiya.

Solskjaer ya ce: "Sun ['yan wasan biyu] warke sosai."

"Sun bi sahun masu yin atisaye yanzu kuma sun yi duk abin da sauran 'yan wasan suke yi. Ya zuwa yanzu babu wata matsala da suka fuskanta.

"Idan muka koma buga gasa, za mu samu cikakkiyar tawaga inda za mu zabi wanda muke so."

Rashford ya yi fama da ciwon baya tun watan Janairu yayin da Pogba bai buga galibin wasannin da United ta fafata a cikinsu ba na kakar wasa ta bana saboda ciwon kafa.