Odion Ighalo: Mai yiwuwa dan wasan zai koma China daga Man Utd

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Odion Ighalo ya shirya komawa China idan zaman aron da yake yi Manchester United ya kare ranar 31 ga watan Mayu, domin har yanzu Shanghai Shenhua da United basu cimma matsaya kan tsawaita zamansa ba.
United ta karbo aron dan wasan na Najeriya, mai shekara 30, a watan Janairu domin maye gurbin Marcus Rashford, wanda yake jinya.
Sai dai saboda barkewar annobar korona, zaman aron da Ighalo yi zai kare kafin a kammala gasar Premier a watan Yuni, kuma a lokacin ne ake sa ran Rashford zai warke sosai ya koma tamaula.
Da ma dai United ta riga ta yanke shawara cewa ba za ta sayi Ighalo dindindin ba, ko da yake bata yanke kaunar tsawaita zamansa na kankanen lokaci ba.
Kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer yana son Ighalo ya ci gaba da zama zuwa karshen kakar wasan bana, ganin cewa suna fafatawa a gasa uku kuma mai yiwuwa su buga wasa 18 cikin wata biyu.
Ighalo, wanda ya dade yana kaunar buga tamaula a United, ya zura kwallo hudu a wasa takwas da ya buga wa kungiyar, kuma yana son ci gaba da zama a Old Trafford idan akwai yiwuwar hakan.
Sai dai yarjejeniya tsakanin United da Shanghai kan ci gaba da zaman dan wasan ta ci tura don haka kungiyar da ke buga gasar Chinese Super League ta dage cewa dole dan wasan ya koma can kamar yadda aka tsara tun da farko.
Makon jiya Ighalo ya koma atisaye a United kuma an fahimci cewa zai je Carrington a wannan makon domin duba yiyuwar ci gaba da zama a kungiyar.











