Kasuwar musayar 'yan ƙwallo: Makomar Allan, Todibo, Henderson, Coutinho, Icardi

Asalin hoton, Getty Images
Everton ta bayar da £40m domin sayo Allan, dan shekara 29, amma Napoli tana so ta sayar da dan wasan na Brazil a kan kusan £60m. (Il Mattino - in Italian)
Kazalika Everton ta ware £25m domin sayo dan wasan Barcelona dan kasar Faransa Jean-Claire Todibo, mai shekara 20, wanda yake zaman aro a Schalke. (Mail)
MamallakinBournemouth Maxim Demin ya kusa sayar da kungiyar ga wata gamayyar 'yan kasuwar Saudiyya a watan Janairu, amma cinikin ya rushe sakamakon rashin amincewa kan farashin kungiyar. (90min)
Manchester United za ta bar golan Ingila Dean Henderson, dan shekara 23, ya kammala kakar bana wacce za ta kare a watan Yuni a kungiyar da ke aronsa Sheffield United. (Telegraph)
Mai yiwuwa dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekara 27, ba zai sake buga wasa a Bayern Munich bayan kungiyar wacce ta karbi aronsa ta yanke hukuncin ƙin sayensa dindindin daga Barcelona kuma an yarda Chelsea, Arsenal ko kuma Tottenhamsu dauke shi. (Sky Sports)
Dan wasanInter Milan da Argentina Mauro Icardi, dan shekara 27, yana dab da zama dan wasan dindindin naParis St-Germain wacce za ta saye shi a kan £54m. (ESPN)







