Arsenal 'za ta ɗauko Coutinho, PSG za ta sayo Pierre-Emerick Aubameyang'
Arsenal za ta soma tattaunawa da wakilin dan wasan tsakiya na Barcelona Philippe Coutinho. Dan wasan dan kasar Brazil mai shekara 27 ya kwashe kakar wasan bana yana zaman aro a Bayern Munich amma kungiyar da ke buga Gasar Bundesliga ta ce ba za ta biya £105m domin daukarsa dindindin ba. (Le10sport - in French)
Paris St-Germain tana tattaunawa da Arsenal a yunkurin dauko Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 30, wanda za a sayar a kan £34m. (Todofichajes)
Dan wasan Juventus Gonzalo Higuain, mai shekara 32, zai iya komawa Gasar Premier bayan rashin jin dadin zaman aro a Chelsea - Newcastle da Wolves suna son dauko shi. (Express)
Rahotanni masu karfi sun nuna cewa dan wasanRB Leipzig Timo Werner, mai shekara 24, zai koma Liverpool amma tsohon dan wasan Manchester United Owen Hargreaves ya ce zai fi kyau idan ya koma Old Trafford. (Star)
Manchester United, Arsenal da kuma Real Madridsuna sanya ido kan dan wasanWolves Raul Jimenez, mai shekara 29 wanda za a sayar a kan £57m.(Tuttosport - in Italian)
Kungiyoyi hudu cikin shida da ke saman teburin Premier suna zawarcin dan wasan Bournemouth Joshua King, dan shekara 28, bayan an ki amincewa da £20m da Manchester United ta so biya a kan dan wasan a Janairu. (Mirror)
Juventus tana so ta doke Real Madrid a gogayyar da suke yi na sayo dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, dan shekara 19, a kan £67m. (Tuttosport - in Italian)
Barcelona ta shirya sayar da dan wasan Faransa Ousmane Dembele, 23, a kan £37m kacal. Kungiyar ta sayo dan wasan a kan £137m shekara uku da suka gabata amma sau biyar kawai ya buga wasa inda ya sha shafa da jinyar raunukan da ya yi ta ji. (Mirror)
Tsohon dan wasan Sheffield United Michael Brown ya bai wa dan wasa Adama Traore, mai shekara 24, ya yi watsi da tayin da Liverpool ta yi masa na komawa can, yana mai kira a gare shi ya ci gaba da zama a Wolves zuwa kakar wasa ta baɗi (Star)
Dan wasan Wales da FC Schalke Rabbi Matondo, dan shekara 19, ya ce yana shirye ya ci gaba da bayar da himma a kungiyar a daidai lokacin da ake rade radin cewa zai koma Manchester United. (Manchester Evening News)











