Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Umtiti, Koulibaly, Pjanic, Haaland, Rabiot

Barcelona ta rage darajar dan wasan Faransa mai shekara 26 Samuel Umtiti zuwa £27m, a yayin da Manchester United da Arsenalsuke son dauko dan wasan. (Sport - in Spanish)

United ta mayar da hankali wurin dauko 'yan wasan baya a bazara, kuma yanzu kocinta Ole Gunnar Solskjaer ya samu damar dauko dan wasan Napoli mai shekara 28 dan kasar Senegal Kalidou Koulibaly, a yayin da Paris St-Germain ta janye daga zawarcinsa. (Express)

Dan wasanJuventus da Bosnia-Herzegovina Miralem Pjanic, mai shekara 30, ba zai amsa tayin komawa Gasar Premier a bazara ba, a yayin da Chelsea take cikin kungiyoyin da suke son dauko shi. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Za a iya tilasta waReal Madrid da Manchester United su jira tsawon shekara biyu kafin su dauko dan wasan Borussia Dortmund, dan shekara 19, Erling Haaland, domin kuwa ba za a yi wa dan wasan na Norway kudi ba, wato euro 75m sai shekarar 2022. (Evening Standard)

Arsenal tana shirin kashe £25m domin karbo dan wasan Dortmund dan shekara 24 dan kasar Switzerland Manuel Akanji, bayan su soma tattaunawa a wata Janairu. (Sun)

A gefe guda, Arsenal ta bi sahun Everton wajen zawarcin dan wasan Juventus dan kasar Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 25, kuma tana fatan zai yi abota da Matteo Guendouzi, mai shekara 21. (Le10 Sport - in French)

Dan wasanTottenham Hotspur dan shekara 29 Danny Rose, wanda yake zaman aro a Newcastle United, ya bayyana cewa yana son murza leda tare da kocin Leicester City Brendan Rodgers - ko da yake cikin raha ya ce sai "an soma sayo" dan wasan Foxes dan kasar Ingila Ben Chilwell, mai shekara 22. (Mail)

Paris St-Germain tana ci gaba da son dauko dan wasan Arsenal dan shekara 30 dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, wanda shekara daya ta rage kafin kwangilarsa a Emirates Stadium. (Le10 Sport - in French)

Leicester tana gaban Manchester City, Wolverhampton Wanderers da kuma Everton a yunkurin dauko dan wasan Celtic da Norway Kristoffer Ajer, mai shekara 22. (90min.com)

Dan wasanDortmund da Jamus Emre Can, dan shekara 26, ya ce ba zai taba komawa Manchester United saboda "zuciyata ba za ta bar ni na koma can ba" bayan ya buga tamaula a Liverpool. (Bild, via Mirror)