Roberto Martinez ya tsawaita kwantiraginsa da Belgium zuwa 2022

Kocin tawagar kwallon kafar Belgium, Roberto Martinez ya tsawaita yarjejeniyarsa zuwa bayan gasar cin kofin duniya da za a yi a 2022.

Dan kasar Spaniya ya karbi aikin jan ragamar Belgium a 2016, inda kwantiraginsa zai kare a karshen gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020.

Sai dai kuma an dage gasar Euro 2020 zuwa shekarar badi saboda tsoron yada cutar korona, yayin da ake sa ran buga gasar kofin duniya a Qatar cikin watan Nuwambar 2022.

Tawagar Belgium ta kare a mataki na uku a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, karkashin Martinez tsohon kocin Everton da Swansea da kuma Wigan.

Belgium ita ce ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a taka leda a duniya, ta kuma ci wasa 10 da ta buga a neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020.

An kuma hada Belgium a rukuni na biyu da ya hada da Denmark da Finland da kuma Russia.

Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasanni don gudun yada cutar korona.