Messi: Sai mun tashi tsaye idan muna son gasar zakarun Turai

Lionel Messi ya ce kungiyar Barcelona ba za ta iya lashe gasar zakarun Turai a bana ba, har sai ta kara azama.

Kafin a dakatar da gasar saboda annobar korona, Barcelona na shirin yin bugu na biyu tsakaninta da Napoli a zagaye na biyu - bayan sun tashi kunnen doki a bugun farko.

A cewarsa Messi, a yadda salon wasansu yake a yanzu, da kamar yuwa su iya lashe gasar.

Dan wasan ya shaidawa jaridar Sport ta Spaniya cewa 'Ina da shakku a kan tawagarmu a gasar zakarun Turai saboda yadda muke murza leda a yanzu.'

A gasar La liga kuwa - Barca na gaban Real Madrid a saman tebur da bambamcin maki biyu kafin a dakatar da gasar.