Bundesliga ta amince kungiyoyi su sauya 'yan wasa biyar

Asalin hoton, Getty Images
An amince wa kungiyoyin Bundesliga su sauya 'yan kwallo biyar, idan aka ci gaba da wasannin bana, bayan da cutar korona ta haddasa tsaiko.
Haka kuma hukumar da ke kula da wasannin Bundesliga ta cimma yarjejeniya da kungiyoyin cewar wadanda suka yi na karshe bayan kammala kakar 2019-20 za su fadi zuwa karamar gasar.
Bundesliga za ta zama ta farko da za a ci gaba da wasanni a nahiyar Turai, tun bayan da aka dakatar da wasanni cikin watan Maris.
Mahukuntan na fatan a karkare sauran wasannin da suka rage na shekarar nan ranar 30 ga watan Yuni zuwa farkon makon Yuli, domin a samu wadanda za su wakilce ta a gasar Zakarun Turai.
Za a yi wasannin ne ba tare da 'yan kallo ba, an kuma dauki matakai na ganin ba a yada cutar korona ba, haka ma a ranar Asabar za a ci gaba karamar gasar Bundesliga.
Kwamitin shugabannin kwallon nahiyoyi ne na Fifa ya amince da sauya 'yan wasa biyar a lokacin wasa don sauwake wa 'yan kwallon gajiya, ganin za su yi wasanni da yawa kuma daf da daf.
Hakan zai sa Jamus za ta zama gasa ta farko da za ta yi amfani da wannan dokar da ake sa ran za ta kare a karshen shekarar nan, kuma tun farko bai zama wajibi ga kasashe ba.







