Coronavirus: Watakila a ci gaba da wasannin La Liga cikin watan Yuni

Barcelona's Arturo Vidal arrives at the club's training ground wearing a mask and gloves for a coronavirus test

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan wasan Barcelona Arturo Vidal lokacin da ya isa wurin atisayen kungiyar sanye da takunkumi da safar hannu domin gwajin cutar korona

Shugaban gudanar da gasar La Liga, Javier Tebas ya ce watakila a ci gaba da wasannin bana daga 12 ga watan Yuni, amma sai an yi gwajin cutar korona ga kowanne dan wasa.

A makon jiya mahukuntan gasar suka fara gwajin 'yan wasa a kokarin da take yi na karkare kakar 2019-20 ba tare da 'yan kallo ba.

A lokacin gwajin ne hukumar ta sanar cewar ta samu 'yan kwallo biyar da ke buga babba da karamar gasar Spaniya dauke da cutar korona.

Koda yake ba a bayyana sunan 'yan wasan ba, amma tuni aka killace su.

Tebas ya ce za a fara karamar gasar Spaniya tare da ta La Liga a lokaci daya, kuma yana sa ran a karkare wasannin bana ranar 31 ga watan Yuli.

Hakan zai bai wa La Liga damar samun zakarun da za su wakilce ta a gasar Zakarun Turai ta badi.

A cikin watan Agustan shekarar nan ake sa ran buga wasan karshe a Champions League a Instambul.

Spaniya tana daga cikin kasar da cutar korona ta yi wa illa a nahiyar Turai, inda mutum 264,663 suka kamu da cutar ta kuma hallaka 26,621 zuwa 11 ga watan Mayu.