Coronavirus: Watakila a ci gaba da wasannin La Liga cikin watan Yuni

Shugaban gudanar da gasar La Liga, Javier Tebas ya ce watakila a ci gaba da wasannin bana daga 12 ga watan Yuni, amma sai an yi gwajin cutar korona ga kowanne dan wasa.

A makon jiya mahukuntan gasar suka fara gwajin 'yan wasa a kokarin da take yi na karkare kakar 2019-20 ba tare da 'yan kallo ba.

A lokacin gwajin ne hukumar ta sanar cewar ta samu 'yan kwallo biyar da ke buga babba da karamar gasar Spaniya dauke da cutar korona.

Koda yake ba a bayyana sunan 'yan wasan ba, amma tuni aka killace su.

Tebas ya ce za a fara karamar gasar Spaniya tare da ta La Liga a lokaci daya, kuma yana sa ran a karkare wasannin bana ranar 31 ga watan Yuli.

Hakan zai bai wa La Liga damar samun zakarun da za su wakilce ta a gasar Zakarun Turai ta badi.

A cikin watan Agustan shekarar nan ake sa ran buga wasan karshe a Champions League a Instambul.

Spaniya tana daga cikin kasar da cutar korona ta yi wa illa a nahiyar Turai, inda mutum 264,663 suka kamu da cutar ta kuma hallaka 26,621 zuwa 11 ga watan Mayu.