Ligue 1: An baiwa Paris St-Germain kofin Ligue 1 na 2019-20

An bayyana Paris St Germain a matsayin wadda ta lashe gasar Faransa ta 2019-20, bayan da gwamnatin kasar ke tsoron yada cutar korona.

Gwamnatin Faransa ce ta ce ba za a koma wasanni ba cikin sauri har sai watan Satumba don gudun yada annobar, dalilin da ya sa ta soke wasannin shekarar nan.

PSG ce kan gaba a teburi da tazarar maki 12 da kwantan wasa, a lokacin da aka dakatar da gasar ranar 13 ga watan Maris don gudun yada cutar korona.

A farkon makon nan Firai Ministan Faransa, Edouard Philippe ya sanar da soke kakar wasanni ta 2019-20.

Hukumar kwallon kafar Faransa ta so a ci gaba da wasannin shekarar nan ranar 17 ga watan Yuni, domin karkare kakar bana.

Kungiyar Amiens da ta Toulouse sun fado daga gasar Ligue 1, bayan da suke karshen teburi.

An bayyana Lorient a matsayin wadda ta lashe gasar Ligue 2. Kungiyar tana mataki na daya a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Lens kan a dakatar da wasannin bana.

Babban jami'in gasar French League, Didier Quillot ya ce daga nan zuwa 25 ga watan Mayu za su sanar da hukumar kwallon kafar Turai, Uefa kungiyoyin da za su wakilce ta a gasar Champions da Europa League a badi.